Tinubu Ya Ware Makudan Miliyoyi, Ya Tallafawa Mutanen da Ambaliya Ta Shafa a Kano

Tinubu Ya Ware Makudan Miliyoyi, Ya Tallafawa Mutanen da Ambaliya Ta Shafa a Kano

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bayar da gudunmawar naira miliyan 100 ga wadanda ambaliyar ruwa ta ritsa da su a jihar Kano
  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben 2023, ya ce ya bayar da tallafin ne domin rage radadi ga wadanda lamarin ya shafa
  • Tinubu ya sha alwashin cewa idan ya zama shugaban kasa, zai tabbatar da ganin cewa Najeriya ta zama tushen wadata ga kowa

Kano - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da tallafin naira miliyan 100 ga wadanda ambaliyar ruwa ta ritsa da su a Kano.

Nigerian Tribune ta rahoto cewa Tinubu ya sanar da bayar da tallafin ne a wajen taron cin abincin dare wanda kungiyar yan kasuwa ta Kano ta shirya masa a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan Ya Zama Dan Gudun Hijira, In Ji Gwamnan Bayelsa

Bola Tinubu
Tinubu Ya Ware Makudan Miliyoyi, Ya Tallafawa Mutanen da Ambaliya Ta Shafa a Kano Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tinubu ya ce ya bayar da tallafin ne domin rage radadi ga wadanda lamarin ya ritsa da su a kananan hukumomin jihar.

Ya kuma yi kira ga dagewa da addu’a da nufin Allah ya kawo karshen annobar ambaliyar ruwa a jihar da ma kasar baki daya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dan takarar shugaban kasar ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta dauki matakai daban-daban don gina ababen more rayuwa da kuma inganta hanyar saukaka yin kasuwanci a fadin kasar.

Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya dauki alkawarin cewa idan aka zabe shi, zai tabbatar da ganin cewa Najeriya ta zama tushen arziki ga kowa, rahoton TheCable.

Ya ce:

“Hadin kai, zaman lafiya da wadata sune manufata a wannan takara.”

Har ila yau, Tinubu ya yi alkawarin sauya fasalin masana’antun da ke jihar tare da mayar da su tushen ci gaba ba wai a arewa ko Kano kawai ba, harma ga fadin kasar.

Kara karanta wannan

Kamfen 2023: Tinubu ya yi magana mai girma game da bashin da ake bin Najeriya

Ya kuma jinjinawa Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar kan jajircewarsa wajen kawo ci gaban ababen more rayuwa.

Tinubu wanda ya bayyana Ganduje a matsayin aboki ya ce akwai alaka mai karfi tsakanin Kano da Lagas tun a shekarun baya saboda kamanceceniyar da ke tsakanin manyan jihohin biyu masu karfin tattalin arziki.

Dan takarar na APC kuma yi wa yan kasuwar alkawarin samar da yanayin da zai taimaka wajen bunkasa harkokin kasuwanci a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng