2023: Magudin Zabe Zai Yi Wahala, An Bayyana Shirin Da INEC Ta Yi

2023: Magudin Zabe Zai Yi Wahala, An Bayyana Shirin Da INEC Ta Yi

  • Mike Igini, tsohon kwamishinan INEC a jihar Akwa Ibom ya ce yan siyasa da ke shirin yin magudi a zaben 2023 za su sha mamaki
  • Igini ya ce hukumar zaben ta samu damar bullo da sabbin na'urori da dabaru don dakile kafafen da yan siyasa ke amfani da su wurin magudi
  • Ya ce an samu damar yin wannan canje-canjen ne saboda rattaba hannu kan sabuwar dokar zabe da Shugaba Buhari ya yi a watan Fabrairun wannan shekarar

Akwa Ibom - Tsohon kwamishinan hukumar zabe INEC, a Jihar Akwa Ibom, Mike Igini, a jiya ya ce yan siyasa da ke fatan za su yi magudi za su sha mamaki a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.

Igini, wanda ya yi magana a shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels ya ce matakan da INEC ta dauka sakamakon amincewa da sabuwar dokar zabe zai bawa masu shirin yin magudi mamaki.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Halaka Dan Sanda Da Wasu 22 Sannan Suka Kona Gidaje 50 A Wata Jahar Arewa

Mike Igini
Zai Yi Wahala Yan Siyasa Su Iya Magudi A Zaben 2023, Igini. @VanguardNGA.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce zaben 2023 zai kafa tarihi a zabukan Najeriya saboda INEC da bullo da sabbin kayan aiki da mutane ba su sani ba.

A cewarsa:

"Mutane nawa suka sani cewa INEC na bibiya yayin zabe kuma a halin yanzu da muke magana bayan rattaba hannu kan dokar zabe a ranar 25 ga watan Fabrairun wannan shekarar, a ranar 26 INEC ta tafi ofis ta yi canje-canje don dacewa da dokar zaben na yanzu. Yan siyasa da dama za su sha mamaki a 2023."

An canja sashi na 40 na dokar zaben 2002 da masu magudi ke fakewa da shi, Igini

Igini ya ce an sauya sashi na 40 na dokar zaben 2002 da sashi na 49 da suka ce idan mai jami'in zabe ya gamsu da mai zabe yana iya barin shi ya kada kuri'a, ana amfani da wannan wurin magudi.

Kara karanta wannan

2023: Da Ace Ni Ba Dan PDP Bane, Da Zan Taimaki Peter Obi Ya Zama Shugaban Kasa, Gwamnan Arewa

Ya ce:

"Sashi na 47 ta bawa INEC damar amfani da na'urar card reader da wasu fasahar da za su tantance mai zabe wanda a baya babu su.
"Yau, mutane su sani idan ka tafi rumfar zabe, babu maganar incident fom, babu maganar zabe na manuwal amma yanzu akwai sabon tsari na 'bimodal'."

Wadanda suka tara katin zabe da yawa ba su iya amfani da shi ba

Igini ya kuma cea sashi na 47 ne dalilin da yasa mutanen da suka tara katin zabe na sata ba za su iya amfani da su ba, suna ta zubarwa.

Ya ce:

"Suna zubar da PVC don saboda sashi na 47 ya magance sashi na 49 da ake amfani da shi a baya ana magudi. Karkashin sabon tsarin, duk wadanda suka boye katin PVC na INEC ba za su iya amfani da shi ba."

INEC Ta Damu Matuka da Rikicin da Ake Samu a Wuraren Yakin Neman Zabe, Ta Gargadi Jam’iyyu

Kara karanta wannan

Saura Wata 7 a Bar Ofis, Buhari Ya Fadawa Ministoci Su Fara Shirye-Shiryen Mika Mulki

A wani rahoto, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana kaduwa da damuwa game da abubuwan dake faruwa na rikici tsakanin jami'iyyun siyasa a fadin kasar nan.

Hukumar ya damuwa da yadda magoya bayan jam'iyyun siyasa ke yin kare jini biri jini a lokutan da suke yawon gangami a Najeriya, rahoton Punch.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164