Budurwar da Ta Rubuta JAMB Sau 7 Ta Kammala Jami’a, Jama’a Sun Taya Ta Murna
- Wata 'yar Najeriya mai suna Mbagwu Amarachi Chilaka ta yi nasarar kammala digiri a jami'ar jihar Imo bayan fafutuka da yawa
- Budurwar mai shekaru 27 ta rubuta jarrabawar JAMB sau bakwai, ta yi karatun sharar fagen shiga jami'a, sannan ta yi diploma
- Amarachi ta bayyana cewa, akwai lokacin da ta ji kamar ta cire rai da yin digiri, amma kullum iyayenta ke ba ta kwarin gwiwa, gashi yanzu ta gama
Burin budurwa mai shekaru 27, Mbagwu Amarachi Chilaka ya cika bayan da ta kammala digirinta a jami'ar jiha ta Imo bayan shafe shekaru tana neman gurbin shiga jami'a.
Da take yada hotunan shagalin kammala karatunta a shafin Facebook, Amarachi ta bayyana cewa, ta yi jarrabawar JAMB sau bakwai, ta yi diploma, ta yi karatun sharar fagen shiga jami'a kafin ta samu gurbin karatu.
Bayananta sun bayyana cewa, ta karanta ilimin tarihi da hulda tsakanin kasa da kasa, daga nan ta godewa Allah bisa wannan gata.
Me yasa take sake rubuta JAMB duk da faduwa da take?
Da take bayyana dalilinta na ci gaba da rubuta JAMB, budurwar wacce marubuciyar intanet ta SEO ce ta shaidawa wakilin Legit.ng cewa, iyayenta ne ke kara ba ta kwarin gwiwa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A kalamansa:
"Da fari dai, mahaifina ne wanda ya tsaya tsayin daka don ganin na tafi makaranta. Bai yi karatun jami'a ba, amma yana matukar son 'ya'yansa su yi.
"Sai mahaifiyata. A duk shekarar da JAMB suka fara siyar da fom, sai in ji na cire rai; takan tabbatar min cewa idan na gwada zan yi nasara."
Ta kuma bayyana cewa, gogewar ta da zaman jami'a ya ba ta damammaki da dama, wannan yasa ta ci gaba da kokarin ganin ta cimma burinta.
Game da kammala karatunta, ta ce dama babban mafarki da burin rayuwarta shine ta yi digiri, kuma yanzu da ta kamma ta cika burinta.
Martanin jama'a
Walson Paladio yace:
"Ina taya ki murna 'yar uwa. Kin cimma wannan burin da kika cancance shi."
Eniola Ennmae Adeniji yace:
"Ina taya ki murna kyakkyawa."
Maazi Obinna Uzodinma Akuwudike yace:
"Ina matukar taya ki murna 'yar uwa.
Lucinda Adanma Akuechiama yace:
"Ina taya ki murna, ina miki fatan alheri."
Bidiyon Yadda Wani Mutum Ya Haukacewa Banki Saboda an Cire Kudinsa Daga Asusu
A wani labarin, wani bidiyon dan Najeriya da ya tada zaman lafiyan banki ya yadu a kafar sada zumunta, an ga lokacin da yake bayyana bacin ransa.
Ba a dai san dalilin da yasa mutumin ya girgiza bankin ba, amma wasu na tunanin ba zai rasa nasaba da cire masa kudi daga asusunsa.
Babbar yarinya: Bidiyon budurwar da ta taso daga Landan za ta dawo Najeriya saboda an janye yajin ASUU
A bidiyon da aka yada gajere, mutumin ya cire rigarsa, ya zauna dirsham kan dandamalin banki inda yake caccakar ma'aikatan da bankin su kuwa suna kallonta.
Asali: Legit.ng