Yadda Matar Aure Ta Zama Mai Aikin Goge-goge Don Tura Mijinta Makaranta A Kasar Waje, Bidiyon Ya Yadu
- Wani magidanci da ke zaune a kasar waje ya fito fili ya nuna rawar ganin da matarsa ta taka don taimaka masa a Kanada
- A wani bidiyo da ya yadu a TikTok, mutumin magantu kan yadda sahibar tasa ta zama mai aikin goge-goge don tura shi makaranta
- Bidiyon ya haddasa cece-kuce inda sauran masu amfani da TikTok suka bayyana ra’ayoyinsu
Wani bidiyon TikTok ya nuno wani magidanci yana kwararo ruwan yabo ga matarsa kan tura shi makaranta da tayi.
Shafin @diandersons ne ya wallafa bidiyon sannan ya hasko mutumin yana cewa matarsa ta zama mai aikin goge-goge don ganin ya samu ingantaccen ilimi.
Ya jinjinawa duk matan kirki da suka tallafawa iyalinsu sannan ya sarawa matarsa.
A nata bangaren, matar ta fadama mutumin da ke mata tambayoyi cewa don tsira a rayuwa, dole sai mutum ya ci abinci kuma don cin abinci dole sai mutum ya yi aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aiki a bangarenta ya hada da zama mai goge-goge don samun madogara idan lokacin haihuwa ya zo.
Bidiyon ya taba zukatan mutane da dama a TikTok yayin da mutane suka yi martani masu dadi. Da dama sun nuna sha’awarsu ga ma’auratan.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
@MarvelousMargz ya ce:
"Ina fatan ba za ka taba y da hin watsi da hakan ba?"
@faithlynfarquhars0 ta yi martani:
"Dan Allah kada ka ci mutuncinta wannan matar kirkin."
@user1458961448950 ta yi martani:
"Zan yi aikin goge-goge don tura kaina makaranta ba namiji ba. Mijina na aiki sannan yana makaranta."
Kyakkyawar Budurwa Mai Shekaru 38 Ta Bazama Neman Miji A Intanet,Ta Fashe Da Kuka A Bidiyo
A gefe guda, wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya mai suna Princess Mimi ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta koka kan cewa har yanzu bata auru ba duk da yawan shekarunta.
Matashiyar mai shekaru 38 ta wallafa wani bidiyo a TikTok inda ta dungi sharban kuka a cikin wata mota yayin da take fallasa asirin zuciyarta.
Princess ta ce zata cika shekaru 39 a bana, kuma har yanzu bata yi aure ko mallakar da nata na kanta ba kuma bata da wani tsayayye da zai fito neman aurenta.
Asali: Legit.ng