‘Yan Sanda Sun Bindige Masu Garkuwa da Mutane 2, Sun Samo Kudin Fansa N8.4m a Bauchi
- Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da halaka wasu mutum biyu da ake zargi da garkuwa da mutane bayan musayar wuta da aka yi dasu a Maina-Maji
- Rundunar ta damke wani matashi mai suna Abubakar Isah mai shekaru 20 da kudi har N8.4 miliyan na fansa da ya karba daga wadanda ya sace
- Har ila yau, ‘yan sandan sun kama makamai masu tarin yawa daga miyagun da suka hada da ‘yan fashi da makami, ‘yan daba da sauransu
Bauchi - Wasu da ake zargi da zama masu garkuwa da mutane har su biyu sun sheka lahira sakamakon musayar wuta ne da suka yi da jami’an ‘yan sanda a kauyen Maina-Maji dake karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi.
Har ila yau, ‘yan sandan sun damke wani matashi mai shekaru 20 mai suna Abubakar Isah da zargin garkuwa da mutane dauke da N8.4m da ake zargin kudin fansa ne ya karba daga jama’a.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Daily Trust ta rahoto cewa, sun samu bindiga kirar SMG dauke da harsasai 92 masu rai, wayoyi guda takwas da sauran makamai.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, CP Umar Mamman Sanda, wanda ya bayyana wadanda ake zargin a ranar Talata a Bauchi yace:
“Halin da tsaron yankunanmu ke ciki ya zama abun damuwa ganin yadda laifuka irinsu daba, fashi da makami, garkuwa da mutane da sauransu. Wannan ne ya zama dole mu sake duba tsarin tsaronmu da kalubalen da ke addabar jiharmu.”
Ya kara da cewa:
“A ranar 7 ga watan Satumban 2022, tawagar sintiri dake Maina-Maji tare da hadin guiwar ‘yan sa kai sun kai samame maboyar masu garkuwa da mutane.
“Bayan isarsu, ‘yan sanda sun budewa masu garkuwa da mutanen wuta inda yayin mayar da martani aka halaka masu garkuwa da mutanen biyu a take.”
CP Sanda ya bayyana cewa, a ranar 23 ga watan Augusta, tawagar jami’an tsaro dake aiki da rundunar sun kama wasu wadanda ake zargi da garkuwa da mutane, fashi da makami da satar shanu wadanda suka addabi Alkaleri, Dass, Tafawa Balewa, Bagoro da Toro da wasu sassan jihar Filato.
Yan Sanda Sun Kama Masu Garkuwa da Mutane 18, Sun Kwato Makamai a jihar Benuwai
A wani labari na daban, dakarun hukumar yan sanda reshen jihar Benuwai sun yi ram da ƴan bindiga masu garkuwa da mutane su 18 kuma sun kwato wasu makamai a hannun su.
Mai magana da yawun hukumar yan sandan, Anene Sewuese Catherine, ita ce ta tabbatar da wannan nasarar ranar Litinin, kamar yadda rahoton Channels tv ya tabbatar.
Asali: Legit.ng