ISWAP Sun Fara Kafa Sansanoninsu a Yankunan Zamfara, Gwamnatin Jiha ta Koka
- Gwamnatin jihar Zamfara tayi korafi kan yadda ‘yan ta’addan ISWAP suke kafa sansanoninsu a yankunan jihar Zamfara da kewaye
- Gwamnatin jihar ta bayyana cewa sansanonin ISWAP sun Suna yankunan kauyen Mutu dake yankin Mada a karamar hukumar Gusau ta jihar
- Har ila yau, ‘yan ta’addan sun gama zana yadda zasu kai miyagun farmaki Danjibga da Kunchin Kalgo a karamar hukumar Tsafe ta jihar
Zamfara - Mambobin kungiyar ISWAP an gano suna kafa sansanoni a wuraren kauyen Mutu dake yankin Mada ta karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara.
Daily Trust ta rahoto cewa, kwamitin gurfanarwa na laifukan da suka hada da ‘yan bindiga da mambobin kwamitin tsaro da sirri, Dr Sani Shinkafi ya bayyana hakan a wani taro a Gusau.
Wani Gwamna Ya Umurci Dalibai Da Ma’aikatan Gwamnatin Jiharsa Su Fara Sanya Kayan Gargajiya Ranar Juma’a
Yace mambobin ISWAP sun shiga jihar ta yankin Danjibga zuwa Kunchin Kalgo a karamar hukumar Tsafe ta jihar inda ya kara da cewa daruruwan ‘yan ta’addan sun gama zana yadda zasu kai farmaki garuruwa da kauyuka a cikin kwanakin nan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yace:
“Mai girma Gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Bello Muhammad Matawalle yayi aiki kan dokar da ya saka hannu inda ya rufe gidajen watsa labarai a jihar. Yayi aiki ne dogaro da sashi na 14 da layi na 2b na kundin tsarin mulkin Najeriya kuma saboda dalilan tsaro.
“Karfin ikon zababbu, ‘yan majalisu da fannin shari’a a bayyane suke a kundin tsarin mulkin Najeriya. A don haka matakin da aka sauka duk na tabbatar da tsaro ne ga jihar sai dai idan kai ba ‘dan Najeriya bane kuma baka son ka gane abinda ake nufi.
“Matakin da gwamnatin jihar ta dauka na tsaro ne ba don hana jama’a hakkin fadin abinda ke ransu ba kamar yadda ake zargi. Tsaron jama’a da kadarorinsu shi ne kan gaba.”
‘Yan Ta’addan ISWAP sun Kai Harin Tsakar Dare Kan Sojoji, Sun Sha Luguden Wuta
A wani labari na daban, Dakarun sojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai sun yi nasarar dakile harin da aka kai musu a daren Litinin a karamar hukumar Mafa dake arewa maso gabashon jihar Borno, Zagazola suka gano.
An tattaro cewa wasu ‘yan ta’adda da ake zargin mambobin ISWAP ne sun tsinkayi garin Borno a motocin yaki da babura inda suka fara kai harin da ruwan wuta a kan dakarun.
Wata Majiyar sirri ta sanar da Zagazola Makama, kwararre a ganni kiyasi da yaki da ta’addanci a tafkin Chadi, cewa dakarun sun bankado harin da ‘yan ta’addan suka kai musu.
Asali: Legit.ng