'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Tsohon Dan Majalisar Dokokin Jihar Anambra

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Tsohon Dan Majalisar Dokokin Jihar Anambra

  • Wasu miyagu sun yi garkuwa da tsohon ɗan majalisar dokokin jihar Anambra, Sylvester Okeke, a kan hanyar Awka
  • Wata majiya daga iyalan ɗan majalisar tace maharan sun kura waya sun nemi a haɗa musu kuɗin fansa kafin suka sako shi
  • Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar yan sandan jihar yace rahoton aukuwar lamarin bai zo ofishinsa amma zai bincika

Anambra - Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon mamba a majalisar dokokin jihar Anambara, Sylvester Okeke, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Bayanai sun nuna cewa Okeke ya shiga hannun masu garkuwa da mutane ne tare da wani mutumi, wanda har yanzu ba'a gano sunansa ba a kusa da shingen binciken Sojoji dake Titin Ring Road, Awka, babban birnin Anambra.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Je Har Babban Masallaci, Sun Yi Awon Gaba da Wani Basarake a Arewacin Najeriya

Harin yan bindiga a Anambra.
'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Tsohon Dan Majalisar Dokokin Jihar Anambra Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

Ance tsohon ɗan majalisar, wanda tun ranar Jumu'a aka daina jin ɗuriyarsa, yana hanyar dawowa daga wurin taron wata ƙungiya a garinsu lokacin da lamarin ya rutsa da shi.

A cewar wata majiya, masu garkuwa da mutanen sun kira iyalan Okeke ta wayar salula kuma sun nemi a tattara musu kuɗin fansa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Majiyar tace, "Shi ne mataimakin shugaban ƙungiyar na ƙasa, bayan kammala taron ya je Shagonsa da ake siyar da Barasa, mun gano cewa yayin da yake kan hanyar komawa Awaka ne aka sace shi."

"Shi kaɗai ne a cikin Motarsa amma su biyu maharan suka sace, mai yuwuwa ɗayan shi ne mai motar da aka gano a kusa da ta tsohon ɗan majalisar, amma har yanzu babu wanda ya gano waye."

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An Halaka Shugaban Matasan Jam'iyyar APC a Wata Jiha

Wata majiyar ta daban daga mahaifar tsohon mamban majalisar, Agulu ƙaramar hukumar Anaocha ta shaida wa yan jarida cewa iyalan Okeke na kokarin shawo kan lamarin a sirrance.

Wane mataki jami'an tsaro suke ɗauka?

Da aka tuntuɓe shi mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, yace basu da masaniya kan faruwar lamarin.

"Rahoton lamarin bai iso kan teburi na ba amma zan bincika sannan na dawo gare ku," inji shi.

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Je Har Babban Masallaci, Sun Yi Awon Gaba da Wani Basarake a Arewacin Najeriya

Yan bindiga sun yi awon gaba da Basaraken kauyen Langai, ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato, Umar Mohammad Zarme.

Rahoto ya bayyana cewa maharan sun bi Basaraken har Masallaci lokacin Sallar Isha'i, suka tare shi kana suka yi gaba da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262