An Gurfanar da Mutumin da Ya Shiga Babban Kanti, Ya Sace Bibul 4
- Wata kotun majistare na tuhumar Godwin Idumu mai shekaru 37 bisa zargin sunkuce bibul 4 masu kimar N72,230 daga wani babban kanti
- An gano yadda aka ga wanda ake karar bidiyon da kamarar CCTV ta nada yayin da yake aikata laifin
- Sai dai, bai amsa laifin ba, lamarin da yasa mai shari’ar ta bada belinsa gami da dage sauran karar zuwa wani lokaci
Legas - Wani mutum mai shekaru 37 mai suna Godwin Idumu ya gurfana gaban wata kotun majistare a Ikeja dake jihar Legas bisa zarginsa da bibul hudu masu kimar N72,230 daga wani babban kanti.
Premium Times ta rahoto cewa, ana tuhumar wanda ake zargin, wanda ‘dan tsaron kanti ne dake zaune a gida mai Lamba 9 Emmanuel St., Maryland dake Lagos da laifin sata.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mai gurfanarwan, Felicia Okwori, ta bayyana wa kotu yadda aka aikata laifukan a 4 ga watan Disambar 2021 da ranar 3 ga watan Yunin 2022 a babban kantin Ebeano dake G.R.A, Ikeja.
Okowori ta ce wanda ake zargin na babban kantin a Disamba, inda ya sunkuce bibul 2 masu kimar N51,080, yayin da aka hango sa ta kamarar CCTV bayan ya bar wurin.
Har ila yau, mai gurfanarwan ta cigaba da bayyana yadda wanda ake zargin a karo na biyu ya sake dawowa ya sace bibul biyu masu kimar N21,150 daga bisani aka yi ram dashi a hanyarsa ta fita.
A cewar mai gurfanarwan, laifukan sun ci karo da dokar sashi na 287 da 411 na kundin laifukan jihar Lagos na 2015.
Sai dai, wanda ake zargin ya musanta aikata laifukan da ake tuhumarsa dasu.
Alkali mai shari’a na kotun majistaren, H.B Magaji ya bada belin wanda ake kara a kan N200,000 da tsayayye daya.
Alkaliya Mogaji ta dage sauraron karar zuwa 25 ga watan Nuwamba.
An gurfanar da wani matashi kan satar Fankar Masallaci a Bauchi, an yanke masa hukunci
A wani labari na daban, an damke wani mutumi mai suna Salisu Aliyu kan zargin satar Fanka a cikin Masallacin garejin motar Dass dake karamar hukumar Dass, jihar Bauchi.
Ba tare da bata lokaci ba an gurfanar da matashin dan shekara 25 gaban kotun Shari'a ta biyu dake jihar, rahoton Leadership.
A kotu, Salisu Aliyu, ya amsa laifin cewa lallai ya aikata wannan laifi.
Asali: Legit.ng