Abin da Zai Kawo Cikas Wajen Bude Jami’o’i da Koyawa Dalibai Inji kungiyar ASUU

Abin da Zai Kawo Cikas Wajen Bude Jami’o’i da Koyawa Dalibai Inji kungiyar ASUU

  • Malaman jami’a sun janye yajin-aikin da suke yi tun farkon shekara, amma har yau akwai sauran aiki
  • Shugaban kungiyar ASUU a Najeriya yace rashin albashi ya sa da-dama ba za su iya zuwa ofishinsu ba
  • Farfesa Emmanuel Osodeke yace mafi yawan malaman suna nesa da jami’a, za su bukaci kudin mota

Lagos - Shugaban kungiyar ASUU ta kasa, Emmanuel Osodeke, ya yi ikirari wasu daga cikin malaman jami’a za su gamu da cikas wajen komawa aiki.

Da aka yi hira da shi a tashar Channels, Farfesa Emmanuel Osodeke yace wasu ‘yan kungiyar ASUU za su sha wahalar zuwa aiki yau saboda rashin kudi.

An tattauna da Farfesan a shirin Sunday Politics domin jin inda aka kwana game da dawowa aiki da malaman jami’a suka yi bayan an yi dogon yajin-aiki.

Kara karanta wannan

Babban Abin da Ya sa Muka Hakura, Muka bude Jami’o’i Bayan Wata 8 inji ASUU

Shugaban na ASUU yace wasu malaman za su yi fama da zuwa jami’o’i domin ba su da kudi.

Malamai ba su da gidaje a makaranta

Daily Trust da ta bibiyi hirar, ta rahoto Osodeke yana mai cewa abubuwa sun canza a zamanin yanzu, mafi yawan malamai su na zama ne a wajen jami’a.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Malaman yake cewa jami’o’i ba za su iya daukar ma’aikata ba, don haka wasu suke rayuwa a wajen makaranta, irin wadannan suna bukatar kudin mota.

Motoci a titi
'Yan ASUU ba su da kudin mota Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Bugu da kari, ‘yan kungiyar ta ASUU sun yi watanni takwas ba a biya su albashinsu ba, don haka zai yi wa wasu malaman wahalar dawainiyar kudin mota.

“A zamanin da, kowane malami yana da gida a cikin makaranta, kuma za ka iya zuwa ofishinka daga gida a kafa.
Amma a zamanin yau, mafi yawan malamai suna zama ne a wuraren da sun kai kilomita 20 ko 30 daga ofishinsu.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: ASUU Ta Jaddada Cewa Har Yanzu FG Bata Biya Mata Bukatunta ba

Ta ya za su biya kudin motarsu zuwa wurin aiki? - Farfesa Emmanuel Osodeke

Gwamnati ta biya bashin albashi - ASUU

BBC ta kawo wannan rahoto, inda aka ji Osodeke yana mai cewa mafita ita ce gwamnatin tarayya ta biya su bashin albashin tsawon watanni takwas.

Idan an biya kudin malamai za su je aji domin koyar da dalibansu, a daidai wannan lokaci sai a cigaba da tattaunawa a kan batutuwan da suka jawo sabani.

Kotu ta sa 'Yan ASUU suka koma aiki

A yau ne aka ji labari Farfesa Emmanuel Osodeke yace ba kokarin Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ba ne ya sa suka koma aikinsu bayan wata da watanni ba.

Shugaban kungiyar malaman jami’an yace har yau ba a cin ma matsaya ba, sai dai ana sa ran gwamnati tayi abin da ya dace tun da sun yi wa kotu biyayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel