Gwamna Ya Bada Sanarwar Dakatar da Sarki Saboda Ana ta Kashe-Kashe a Kasarsa
- Gwamnatin Jihar Ebonyi ta dakatar da Mai martaba Sarkin Isinkwo da ke sarauta a yankin Onicha
- An dakatar da Sarki Josephat Ikengwu ne saboda rikicin da ake tayi a Isinkowo wanda ya ki cinyewa
- Mai girma gwamna David Umahi ya bada wannan sanarwa ta bakin sakataren gwamnatin jiha (SSG)
Ebonyi - Mai girma gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, ya dakatar da Mai martaba Sarkin Isinkwo da ke karamar hukumar Onicha.
Jaridar Vanguard a rahoton da ta fitar a ranar Lahadin da ta gabata, tace an dakatar da Josephat Ikengwu ne saboda kashe-kashen da ake yi.
Ana ta fama da rigingimu a kasar Isinkwo wanda suka yi sanadiyyar mutuwar Bayin Allah.
Gwamnati ta zargi Josephat Ikengwu da cewa ya gaza kawo karshen wannan matsala da take faruwa a kasarsa, don haka ta dauki mataki.
A wata sanarwa da ta fito daga ofishin Sakataren gwamnatin jihar Ebonyi, Dr. Kenneth Ugbala a Abakaliki aka ji cewa an dakatar da Sarkin.
Rahoton yace dakatarwar da aka yi wa Basaraken za ta fara aiki ne ba tare da wata-wata ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN tace a matsayin Sarki, Dr. Kenneth Ugbala ya zarge shi da gaza yin abin da ya kamata a Isinkwo.
Ana sa ran zuwa yau Basaraken zai tattara duk wasu dukiyoyin gwamnati da suke fadarsa, ya maida su ga Sakataren gwamnati na jihar Ebonyi.
"Saboda haka, zai dawo da duk kayan gwamati da ke hannunsa, har da motar aikinsa ga Sakataren gwamnati jiha kafin a tashi aikin ranar Litinin 17 ga watan Oktoba, 2022 ko kafin ranar.
- Dr. Kenneth Ugbala
Sarakuna suna rasa rawaninsu
Ba wannan ne karon farko da aka ji Gwamna ya dakatar ko ya tsige Sarki a shekarar nan ba, a wasu lokutan kuma kotu ke cirewa Sarakuna rawani.
Kwanakin baya Gwamna Ben Ayade ya sauke Sarkin Kalaba, Farfesa Itam Hogan Itam saboda ana zargin Mai martaban yana shiga harkar siyasa.
Ambaliya a Bayelsa
Kun samu labari cewa a halin yanzu Bayelsa tana fuskantar mafi munin ambaliyar ruwan sama da aka gani a cikin akalla shekaru 10 da suka wuce.
Gwamna Douye Diri yace ruwan damina ya jawo hanyoyi sun datse, mutane a garuruwa da-dama suna rayuwa a dar-dar da matsanancin yunwa.
Asali: Legit.ng