Gwamnan PDP, Fayose Da Wasu Masu Fada Aji Sun Halarci Bikin Rantsar Da Sabon Gwamnan APC

Gwamnan PDP, Fayose Da Wasu Masu Fada Aji Sun Halarci Bikin Rantsar Da Sabon Gwamnan APC

  • Ekiti ta yi cikar kwari yayin da aka yi bikin rantsar da sabon gwamnan jihar Mista Abiodun Oyebanji
  • Daga cikin wadanda suka halarci bikin rantsar da gwamnan na APC harda tsohon gwamnan jihar Ayodele Fayose da Gwamna Godwin Obaseki na PDP
  • Da yake daukar rantsuwar kama aiki, sabon gwamnan ya sha alwashin ciyar da jihar Ekiti gaba tare da kawo zaman lafiya a cikinta

Ekiti - Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose suna cikin manyan masu fada aji da suka halarci bikin rantsar da sabon gwamnan jihar Ekiti, Mista Abiodun Oyebanji, rahoton Vanguard.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, tsohon gwamnan jihar Ekiti, Niyi Adebayo, tsohon shugaban APC kuma tsohon gwamnan jihar Osun, Cif Bisi Akande duk sun halarci bikin rantsarwar.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Wike Ya Dauki Ortom, Makinde Da Ikpeazu Sun Shilla Kasar Waje, An Bayyana Dalilin Fitarsu

Bikin rantsar da Oyebanji
Gwamnan PDP, Fayose Da Wasu Masu Fada Aji Sun Halarci Bikin Rantsar Da Sabon Gwamnan APC Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Da yake jawabi a taron, Abiodun Oyebanji ya dauki alkawarin inganta jihar Ekiti tare da kawo damammaki, zaman lafiya da kuma ci gaba.

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Hangena shine jihar Ekiti ta zama kasa mai wadata, mai damammaki, zaman lafiya da ci gaba. Kasa wacce mutane da al’ummar cikinta zasu girbe abun da suka shuga cikin mutunci, ingantaccen lafiya da aminci. Kasar girma inda ake daraja mutunci. Don ganin wannan mafarki ya zama daidai ya zama dole mu mayar da hankali kan turbar da za ta kaimu wajen.”

Sauran gwamnonin da suka halarci bikin sun hada da Babatunde Sanwoolu na jihar Lagas da Badaru Abubakar da jihar Jigawa.

Yanzu Yanzu: Tsohon Sakataren Gwamnatin Katsina, Mustapha Inuwa, Ya Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP

A wani labarin kuma, tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina karkashin gwanna Amiju Bello Masari mai ci, Dr Mistapha Muhammad Inuwa ya sauya sheka daga jam'iyyar All Progressives Party zuwa Peoples Democratic Party, PDP.

Kara karanta wannan

2023: Daruruwan 'Ya'Yan APC a Mazabar Gwamnan Arewa Sun Sauya Sheka Zuwa PDP

Dan siyasar ya kuma kasance tsohon kwamishinan ilimi a jihar.

Inuwa wanda shine sakataren gwamnati mafi dadewa a jihar ya sanar da sauya shekarsa a ofishin kamfen dinsa a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba, Leadership ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel