'Yan Bindiga Sun Je Har Masallaci, Sun Yi Awon Gaba da Wani Basarake a Jihar Filato
- Yan bindiga sun yi awon gaba da Basaraken kauyen Langai, ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato, Umar Mohammad Zarme
- Rahoto ya bayyana cewa maharan sun bi Basaraken har Masallaci lokacin Sallar Isha'i, suka tare shi kana suka yi gaba da shi
- Mai magana da yawun hukumar yan sandan Filato, ASP Alfred Alabo, yace tuni dakaru suka shiga jeji don kubutar da Basaraken
Plateau - 'Yan bindiga Sun sake garkuwa da wani basaraken gargajiya a jihar Filato, arewa ta tsakiya a Najeriya, kamar yadda jaridar AIT LIVE ta ruwiato.
Maharan sun yi awon gaba da Magajin Garin Langai, Umar Mohammad Zarme da ke yankin ƙaramar hukumar Mangu a jihar Filato.
Bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru ne ranar Asabar 15 ga watan Oktoba, 2022 jim kaɗam bayan sallar Isha'i tsakanin karfe 7:30 zuwa 8:00 na dare a babban Masallacin Langai.
Shugaban Masarautar Fyam, Iliya Manu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya faɗa wa manema labarai cewa ana zargin yan bindigan Fulani makiyaya ne.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yace, "Maharan sun shiga yankin da yawansu, suka tura ɗayansu ya shiga Masallacin wurin basaraken kuma bayan gama Sallah ya biyo bayansa har zuwa wuri mai duhu."
"Ɗaga nan ne suka buɗe wuta a saman iska domin tsorata mutanen ƙauyen kuma suka ankarar da 'yan uwansu domin su fito daga wuraren da suka ɓuya, daga bisani suka yi gaba da shi."
Shin yan bindigan sun tuntubi iyalan Basaraken?
Ya ƙara da cewa masu garkuwan sun tuntubi iyalai ta wayar salulan magajin Garin kuma sun bukaci a haɗa musu miliyan N20m a matsayin kudin fansa.
Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Filato, ASP Alfred Alabo, ya tabbatar da rahoton, inda yace tuni dakaru suka bazama cikin jeji domin binciko maharan.
A.wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Dan Fitaccen Dan Majalisar Dokokin Jihar Sokoto
Wasu yan bindiga da ake zaton masu garkuwa ne sun kashe Ɗan banga a kauyen Rimawa, karamar hukumar Goronyo a jihar Sakkwato.
Maharan sun kuma jikkata wani mutum ɗaya kana suka yi awon gaba da ɗan mamba mai wakiltar Goronyo a majalisar dokokin jihar.
Asali: Legit.ng