Muhammadu Sanusi II: Ina Tausaya Wa Wanda Zai Gaji Buhari

Muhammadu Sanusi II: Ina Tausaya Wa Wanda Zai Gaji Buhari

  • Sanusi Lamido Sanusi, Khalifan darikar Tijanniya ya ce yana tausayin shugaban Najeriya da zai gaji Buhari ya kuma yi yunkurin cire tallafin mai
  • Tsohon sarkin na Kano ya furta hakan ne wurin taro a Kaduna ranar Asabar 15 ga watan Oktoba inda ya ke kokawa kan yawan bashin da ake ciyowa a kasar ana amfani da shi wurin biyan tallafi da harajin bashi
  • Tsohon shugaban babban bankin na kasa ya ce idan kasar ta cigaba da karbo bashin, za ta laftawa masu tasowa bashin da zai fi karfinsu har ta yi wu su rika zagin shugabannin yanzu

Kaduna - Tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi kuma mataimakin shugaban hukumar bunkasa saka hannun jari na Kaduna, ya ce yana tausayin wanda zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari duba da yadda tattalin arziki ta tabarbare.

Kara karanta wannan

Abinda Yasa Nake Da Gwarin Guiwar Cewa Ni Zan Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2023, Tinubu Ya Magantu

Sanusi, wanda kuma shine Khalifa na darijar Tijanniya a Najeriya, ya furta hakan ne a ranar Asabar a Kaduna yayin da ya ke jin jawabi ga yan siyasa a wurin taron da aka yi wa lakabi da "Gina Kwakwaran Tattalin Arziki".

Sanusi
Tallafin Man Fetur: Ina Tausaya Wa Wanda Zai Gaji Buhari, Muhammadu Sanusi II. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sarkin Kanon na 14 ya ce tattalin arzikin kasar ya dogara ne ga man fetur da iskar gas kuma cire tallafi yana kara gurgunta tattalin arzikin, rahoton The Punch.

Ya koka kan yadda Najeriya ta dogara da ciyo bashi kuma wasu tsiraru da ke mulki a kasar ke azurta kansu su zama attajirai cikin dare daya.

Ya ce idan aka cigaba da haka rashin tsaro zai iya tabarbarewa kasar ta zama tamkar Mali da Burkina Faso.

Jihohi 50 cikin 100 ne ke iya samar kudaden da za su biya ma'aikata da biyan harajin bashi

Kara karanta wannan

"Najeriya Na Cikin Halin Yaƙi", Sanatan APC Mai Ƙarfin Fada A Ji Ya Yi Magana Mai Ɗaukan Hankali

Da ya ke bada misali da bayanai daga kwamitin rabon arzikin kasa, Sanusi ya ce jihohi 50 cikin 100 ne kawai a kasar ke iya samar da kudin shiga da za su biya ma'aikata, kudaden gudanarwa da harajin bashi.

Sanusi: Ina jin tausayin shugaban kasa da zai zo bayan Buhari ya ce zai cire tallafi

Wani sashi na jawabinsa:

"Muna bar ya yayan mu tarin bashi. Su (yaran) ta yi wu su rika zagin mu saboda muna amfani da dukkan kudin da aka ranto don biyan tallafin fetur kuma a same shi da sauki.
"Mun ga matsalar muma za mu cigaba. Ina tausaya wa shugaban kasa na gaba da zai zo a watan Yuni ya ce zan tire tallafin man fetur bayan kwana daya."

Sanusi II ya Sanar da Tinubu Cewa Bashi da Jam’iyyar Siyasa, Najeriya ce a Gabansa

A bangare guda, Sanusi Lamido Sanusi a ranar Asabar, ya sanar da ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu cewa bashi da jam’iyyar siyasa.

Kara karanta wannan

Muna Shawaran Sake Ciwo Bashi Daga Wajen Asusun Lamunin Duniya, Ministar Kudi

Channels TV ta rahoto cewa, Sanusi yayi wannan batun a Kaduna yayin da ake gudanar da taron shekara shekara na KadInvest wanda Cibiyar Habaka Zuba Hannayen jari na jihar Kaduna ke shiryawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel