Ayarin Motoccin Kakakin Majalisar Jiha A Najeriya Sun Yi Hatsari, Da Dama Sun Jikkata
- Mummunan hatsari ya faru tsakanin wata mota da motoccin ayarin kakakin majalisar jihar Osun, Mr Timothy Owoeye a Osogbo-Illesha
- Shaidun gani da ido sun ce wata mota ce ta taho ta yi 'taho mu gamu' da wasu motoccin ayarin kakakin majalisar hakan ya yi sanadin jikkatar mutane da dama
- Babban sakataren watsa labaran kakakin na Osun, Mr Akin Alabi ya tabbatar da hatsarin ya ce wadanda suka jikkata suna asibitin UNIOSUN da Asibitin Majalisar Dokokin Osun
Jihar Osun - Wasu mutane cikin motocci, a ranar Alhamis, sun samu raunuka daban-daban a ayarin motoccin kakakin majalisar jihar Osun, Hon Timothy Owoeye, da suka yi hatsarin mota kan hanyar Osogbo-Illesha.
Lamarin da ya faru a ranar Alhamis, an tattaro ya yi sanadin jikkatan mutane da dama da ke cikin motoccin kuma a halin yanzu suna Asibitin Koyarwa na Jami'ar Jihar Osun a Osogbo.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Shaidun gani da ido sun bayyana wa Tribune Online cewa hatsarin ya faru ne saboda motar da ke zuwa ta dayan bangaren titin ta taho ta yi karo da mota da ke tawagar kakakin majalisar.
Mai magana da yawun kakakin majalisar ya yi martani
Mr Kunle Alabi, babban sakataren watsa labarai na kakakin majalisar ya ce hatsarin ya faru ne saboda wata mota ta taho ta yi gaba da gaba da tawagar.
Alabi ya ce an kai wadanda suka jikkata Asibitin Koyarwa na UNIOSUN da Asibitin Majalisar Dokokin Jihar Osun don musu magani.
Yan Ta'adda Sun Kai Wa Ayarin Motoccin Hajiya Zainab Gummi Hari A Zamfara
A wani rahoton, kwamishinan Mata da Harkokin Yara, Hajiya Zainab Lawal Gummi, ta tsallake rijiya da baya a yayin da yan ta'adda suka kaiwa ayarin motoccinta hari, rahoton HumAngle
Yan ta'addan sun bude wuta kan ayarin motoccin uku misalin karfe 6 na yammacin ranar Talata, 30 ga watan Agustan 2022, a Kwanar Dogon Karfe, kan hanyar Sakkwato - Zamfara a karamar hukumar Bakura.
An tabbatar cewa kwamishinan, wacce ke kan hanyarta daga Sakkwato zuwa Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, ta tabbatar da harin amma ta ce lafiyarta kalau.
Asali: Legit.ng