Da Dumi-Dumi: EFCC Ta Sha Kaye Yayin da Kotu Ta Wanke Wani Tsohon Gwamnan Arewa Daga Badakalar N8.3bn

Da Dumi-Dumi: EFCC Ta Sha Kaye Yayin da Kotu Ta Wanke Wani Tsohon Gwamnan Arewa Daga Badakalar N8.3bn

  • Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sanata Saminu Turaki ya yi gagarumin nasara kan hukumar yaki da cin hanci da rashawa a kotu
  • Babbar kotun tarayya da ke zama a Dutse ta wanke Turaki da wasu kamfanoni uku daga tuhume-tuhume 33 da EFCC ke yi masu
  • Mai shari'a Hassan Dikko ya bayar da umurnin mikawa tsohon gwamnan takardun tafiyarsa nan take

Jigawa - Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, ta sallami Sanata Saminu Turaki tare da wanke shi kan tuhumar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ke masa, Punch ta rahoto.

Hukumar EFCC dai na zargin Turaki da aikatan rashawar kudade har naira biliyan 8.3.

Tun a ranar 4 ga watan Mayun 2007 Turaki da wasu kamfanoni uku ke fuskantar shari’a a karar da EFCC ta shigar kan tuhume-tuhume 33.

Kara karanta wannan

Mamaki Yayin Da Gwamnatin Buhari Ta Amince EFCC Ta Gurfanar Ta Shahararriyar Sanatan APC A Kotu

Saminu Turaki
Da Dumi-Dumi: EFCC Ta Sha Kaye Yayin da Kotu Ta Wanke Wani Tsohon Gwamnan Arewa Daga Badakalar N8.3bn Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan a gaban Justis Binta Nyako na babbar kotun Abuja a ranar 13 ga watan Yulin 2007.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai kuma, an mayar da shari’ar zuwa babbar kotun tarayya da ke Dutse a shekarar 2011, bayan tsohon gwamnan ya kalubalanci hukuncin kotun reshen birnin tarayya.

An umurci sabon alkali, Justis Hassan Dikko, da ya karbi ragamar shari’ar wanda a da yake a hannun Justis S. Yahuza kafin yayi ritaya a farkon Disamba.

Alkalin da ke jagorantar shari’ar, Justis Hassan Dikko, wanda ya yanke hukunci, ya soke dukka tuhume-tuhume sannan ya sallami duk wadanda ake zargi a shari’ar.

Kotun ta kuma yi umurnin cewa a saki takardun tafiyar mutum na farko da ake zargi, Saminu Turaki, tare da mika masa su nan take.

Da yake martani kan hukuncin, Saidu Tudunwada, wanda yake daya daga cikin masu kare wadanda ake kara, ya bayyana cewa kotun ta ga inganci a bukatar da suka shigar na neman a sallami wadanda ake kasa daga tuhume-tuhume 33.

Kara karanta wannan

Jami’an Hisbah Sun Kama Mata Masu Yawan Gaske Saboda Kwankwadar Barasa Da Karuwanci A Wata Jihar Arewa

Ya kara da cewar, da wannan hukunci, gaskiya tayi halinta kuma ya kasance nasara ga kowa. rahoton Daily Post.

Bayan shekaru 14, an cigaba da shari'ar wawurar kudaden da tsohon gwamnan arewa ya yi

Mun kawo a baya cewa an cigaba da shari'ar tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sanata Ibrahim Saminu Turaki a babbar kotun tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa, bayan shekaru goma sha hudu.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Turaki ya bayyana a gaban kotun a ranar 7 ga watan Disamba inda ya ke fuskantar zargi 32 kan wawurar wasu kudi da suka kai N36 biliyan.

A shekarar 2007, hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta damke tshon gwamnan kuma ta gurfanar da shi a gaban wata babbar kotun tarayya karkashin jagorancin Mai shari'a Binta Murtala Nyako.

Asali: Legit.ng

Online view pixel