Yan Bindiga Sun Sace Babban Dan Sanda A Jihar Arewacin Najeriya

Yan Bindiga Sun Sace Babban Dan Sanda A Jihar Arewacin Najeriya

  • Wasu yan bindiga da ake zargin masu garkuwa ne sun sace babban jami'in dan sandan Najeriya, Abdulmumini Yusuf a Kwara a unguwar Ogidi
  • Paul Odama, kwamishinan yan sandan Kwara ya ziyarci unguwar, ya kuma ce sun fara farautar maharan da nufin ceto shi da kama su
  • Majiyoyi daga unguwar sun magantu kan yadda lamarin ya faru inda suka ce maharan sun sace shi ne yayin da ya dawo zai shiga gida bayan ya dawo daga aiki

Kwara - Yan bindiga sun sace wani babban jami'in dan sanda mai suna Abdulmumini Yusuf a daren ranar Talata a garin Ogidi a karamar hukumar Ilori ta Yamma a Jihar Kwara.

Abdulmumini wanda aka fi sani da "Emirate No1" a unguwar mataimakin sufritanda ne da ke aiki a rundunar Ilorin, kamar yadda aka tattaro.

Kara karanta wannan

Abun Tausayi: An Gano Wani Bawan Allah Tsirara da Aka Kulle Tsawon Shekara 20 a Kaduna

Taswirar Kwara
Yan Bindiga Sun Sace Babban Dan Sanda A Kwara. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Majiyoyi a unguwar Ogidi sun magantu kan sace dan sandan

A cewar majiyoyi, lamarin ya faru ne a daren ranar Talata yayin da ya ke dab da shiga gidansa a Ogidi bayan an tashi aiki.

Majiyoyi sun shaidawa Punch Metro a ranar Laraba a Ilorin cewa kwamishinan yan sanda, Paul Odama, ya ziyarci unguwar bayan afkuwar lamarin.

Majiyar ta ce:

"Mun ga yan sanda da yawa suna ta sintiri a unguwar sakamakon zuwa kwamishinan yan sandan."

Wani mazaunin unguwar mai suna Jami'u Abdulganiy, ya ce lamarin ya jefa tsoro a zukatan mutane ta yadda za a iya sace dan sanda ba da tsoro ba.

Da ya ke magana kan lamarin, sakataren kwamitin bada shawara na yan sandan unguwa, Shola Muse, ya ce lamarin alama ne da ke nuna karuwar rashin tsaro a jihar.

Kara karanta wannan

Bidiyo: 'Yar Najeriya ta mutu yayin da ake mata tiyatar cikon mazaunai a India

Ya yi kira ga hukumomin tsaro su inganta ayyukansu.

Martanin kwamishinan yan sandan Kwara Paul Odama

Kwamishinan yan sandan Kwara, Paul Odama, ya tabbatar da afkuwar lamarin ya kara da cewa rundunar ta fara bincike ta kuma baza tarkonta don kama maharan da ceto jami'in.

Shugaban yan sandan ya ce:

"Eh, da gaske ne, amma muna aiki a kan lamarin."

Yan Bindiga Sun Sace Yan Sanda Da Tsakar Rana A Jihar Ogun

A wani rahoton, yan bindiga sun sace jami'an rundunar yan sanda uku a Wasinmi, karamar hukumar Ewekoro ta Jihar Ogun.

Daily Trust ta rahoto cewa an sace wadanda abin da ya faru da su ne da rana tsaka kuma sun ziyarci jihar Ogun ne daga Zone 2 Onikan Legas don bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164