Bidiyon Malamin Makarantan da Yaje Banki da 'Ghana-Must-Go' don Karbar Albashinsa na Wata 8 Ya Ba Da Mamaki
- Wani bidiyon da aka yada ya nuna wani malamin makaranta ya je banki a wani yanayin da ba a saba ganin irinsa ba
- Ba tare da nuna wata damuwa ba, an ga malamin dauke da katuwar jaka da ake tunanin a ciki zai zuba kudadensa idan ya cire
- Bidiyon dai ya jawo cece-kuce, mutane da dama a kafar sada zumunta sun bayyana ra'ayoyinsu a kai
'Yan soshiyal midiya sun yi martani ga bidiyon wani mutumin da aka gani a banki dauke da jakar 'Ghana Must Go' rataye a kafadarsa.
A cewar @nanahook00, wacce ta yada bidiyon a TikTok, mutumin malamin makaranta ne, kuma ya zo da jakar ne domin karbar albashinsa na wata takwas da yake bin gwamnati.
A cikin bidiyon mai tsawon dakiku 10, an ga lokacin da malamin ke muzurai a cikin bankin, ya kuma nuna kamar ba komai yayin da yake harkar dake gabansa.
Legit.ng Hausa bata iya tantance gaskiyar cewa da gaske malamin makaranta ne kuma ya zo karbar albashinsa ne ba. An dai bayyana cewa, lamarin ya faru ne a kasar Ghana.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kalli bidiyon:
Martanin jama'a kan bidiyon
Mutane da dama sun yi martani, ga dai abin da suke cewa:
Toto yace:
"Watakila ya zo ne daga Qnet a tunani na."
$FAZ$ yace:
"Na tabbata bankin sun rufe bayan ya cire kudinsa."
Abena Adoma yace:
"Wannan sabon shigan malamin makaranta ne."
Quecu Penzilz yace:
"Kudi mai yawa za mu cire."
Nana Akosua Adobea Koomson yace:
"Don me za su ba shi sulalla wajen biyansa hakkinsa."
Josh yace:
"Yana son tabbatarwa ne yana da wannan adadin kudin, haka ya faru dani nima a 2019, sai da na tambayi mutane 5 don su tabbatar min balas dina zai kai."
Wani Uba ya Fusata, Ya Ce Ba Zai Sake Siyan Kunzugun Jaririnsa Ba Saboda Dalilai
A wani labarin, wani bidiyon magidanci dan Najeriya dake masifa kan yadda matarsa ke sanyawa dansu kunzugun yara ya jawo cece-kuce a shafukan intanet.
An yada bidiyon ne a TikTok, inda aka ga mutumin na luguden lebe kan cewa yakan sayi kunzugun amma ya kare da wuri.
Babatun da yake ya biyo bayan shigo da fakitin kunzugun da ya siyo a kasuwa akan farashi mai tsada.
Asali: Legit.ng