Wani Uba ya Fusata, Ya Ce Ba Zai Sake Siyan Kunzugun Jaririnsa Ba Saboda Dalilai

Wani Uba ya Fusata, Ya Ce Ba Zai Sake Siyan Kunzugun Jaririnsa Ba Saboda Dalilai

  • Mata da miji dake masifa da fada kan adadin kunzugun da matarsa za ta ke sanyawa dansu sun yawo cce-kuce
  • A wani bidiyon da aka yada a TikTok, an ga lokacin da mijin ke nuna fushi da matarsa kan yadda take karar da kunzugun yaron da wuri
  • Bidiyon mai ban dariya ya sa jama'a da dama sun shiga mamaki, wasu sun ba su shawarin yadda ya kamata su yi

Wani bidiyon magidanci dan Najeriya dake masifa kan yadda matarsa ke sanyawa dansu kunzugun yara ya jawo cece-kuce a shafukan intanet.

An yada bidiyon ne a TikTok, inda aka ga mutumin na luguden lebe kan cewa yakan sayi kunzugun amma ya kare da wuri.

Babatun da yake ya biyo bayan shigo da fakitin kunzugun da ya siyo a kasuwa akan farashi mai tsada.

Kara karanta wannan

Rikici: Tashin hankali yayin da kanin miji ya kwace wa dan uwansa mata mai 'ya'ya 7

Magidanci ya fusata da yadda ake wahala shi wajen sayen kunzugun yara
Wani Uba ya Fusata, Ya Ce Ba Zai Sake Siyan Kunzugun Jaririnsa Ba Saboda Dalilai | Hoto: TikTok/@only_rebeka and Eric O'Connell/Getty Images.
Asali: UGC

Daga nan ne ya kafawa matar dokar yadda kunzugun zai dade don rage kashe kudi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yaro dai dole ya yi kashi, inji matar

Sai dai, matar bata yi shuru ba, ta ce masa ai ba laifinta bane don kunzugun yaron ya kare da wuri. Tace tunda yaron na cin abinci, to kuwa dole ya buga kashi saboda al'ada ce ta dan adam.

Bai hakura ba, daga nan ya sake fusata tare da nuna cewa, dole a fara amfani da kunzugu daya a rana a gidansa.

Ya kuma buga gargadin cewa, ba zai ma sake sayen kunzugun ba nan da watanni uku.

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a

Jama'a da dama a karkashin bidiyon sun yi martani, ga abin da wasu ke cewa:

@Flora Smith tace:

"Baka ma fara ba har ka fara korafi."

Kara karanta wannan

Tallafi Na Jiransa: Dan Najeriya Ya Sa A Nemo Masa Mubarak Yusuf, Yaro Makanike Da Ke Zuba Turanci A Bidiyo

@Chinwendu Umeh382 yace:

"Da na da amfani da 5 kafin gari ya waye.

@Amarachi Faith398 tace:

"Wannan lamari na kunzugu ya so ya jawo min matsala a gidana."

@Fikayomi Bright yace:

"Ba zai yiwu ba fa"Da na na amfani da guda 120 a cikin mako uku."

Yadda Kanin Miji Ya Kwace Matar Dan Uwansa Mai 'Ya'ya Bakwai

A wani labarin, wani mutum mai shekaru 56 ya bayyana irin wahalar da yake sha na kula da yara bakwai da matarsa ta bar masa bayan da ta tare da kaninsa.

Simon Murefu Muyeho ya ce, kaninsa dan acaba ne, yakan dauki matarsa Farida a babur har soyayya ta kullu a tsakaninsu.

Yace, yayin da kusancinsu ya yi nisa, Farida ta bayyana soyayyarta ga kaninsa, wanda suka koma zama tare a karkashin rufi daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel