Tsautsayi Ya Ratsa Yayin da Wani Matashi Ya Naushi Abokinsa Ya fadi Ya Mutu a Kano
- Dakarun 'yan sanda sun kama wani matashi ɗan shekara 18 a duniya, Saminu Bala, bisa zargin kashe abokinsa a jihar Kano
- Kakakin hukumar yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, yace saɓani ne ya shiga tsakaninsu, Bala Ya daki Khalil
- Bayanai sun nuna cewa mamacin ya rasa rayuwarsa ne sakamakon dukan da Bala ya masa a Kofar Mazugal, Dala LG
Kano - Hukumar 'yan sanda reshen jihar Kano dake arewa maso yammacin Najeriya ta kama wani matashi ɗan kimanin shekara 18, Saminu Bala, bisa tuhumar kashe abokinsa yayin faɗa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin wanda har ta kai ga rasa rayuwa ya faru ne a Anguwar Kofar Mazugal da ke ƙaramar hukumar Dala a birnin Kano.
Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar 'yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da kama wanda ake zargi ga jaridar City & Crime.
Mai magana da yawun 'yan sandan ya ce mamacin mai suna, Ibrahim Khalil da wanda ake tuhuma, Saminu Bala, sun ɓarke da gardama a tsakaninsu har ta kai ga faɗa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar Abdullahi Kiyawa, yayin wannan sabani da ya kai su ga faɗa ne aka aikata wannan ɗanyen aiki lokacin da Bala ya naushi Khalil, hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa wannan na zuwa ne lokacin da ake ci gaba da shari'a kan Ɗan China, wanda ya daɓa wa budurwarsa, Ummita, wuƙa har lahira a Kano.
Lamarin mai rikitarwa ya ja hankalin mutane da dama, aka yi ta kira ga hukumomi su bi wa marigayya Ummita haƙƙinta.
Gwamnatin Kano zata canza wa KUST Wudil suna
A wani labarin kuma Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da batun sauya wa jmai'ar KUST Wudil suna zuwa Aliko Dangote
Tun a watan Mayu, gwamnatin jihar Kano ta nemi amincewar majalisar na canza wa makarantar suna bayan karɓar shawarwarin wani kwamiti.
Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ne ya kafa jami'ar a shekarar 2001 lokacin mulkinsa na farko.
Asali: Legit.ng