Tsohon Gwamnan Da Buhari Ya Yi Wa Afuwa Ya Fadi Yadda Za'a Kawo Karshen Cin Hanci da Rashawa a Najeriya

Tsohon Gwamnan Da Buhari Ya Yi Wa Afuwa Ya Fadi Yadda Za'a Kawo Karshen Cin Hanci da Rashawa a Najeriya

  • Sanata Joshua Dariye ya ce sai yan Najeriya sun bayar da cikakken hadin kai kafin a iya kawo karshen cin hanci da rashawa
  • Tsohon gwamnan na Plateau wanda shugaba Buhari ya yiwa afuwa ya bayyana cewa akwai masu yiwa manufofin gwamnati zagon kasa
  • Dariye ya ce akwai siyasa a lamarin daure shi da aka yi domin akwai wadanda suka fi sa ta'asa amma aka kyale su

Tsohon gwaman jihar Plateau, Joshua Dariye, ya bayyana cewa za a iya kawo karshen cin hanci da rashawa a kasar nan idan har kowani dan Najeriya zai bayar da hadin kai.

Sanatan ya bayyana hakan ne a a ranar Litinin, yayin wata hira da gidan talbijin din Channels a shirin NewsNight.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan da Aka Daure Yace Obasanjo Ya Ci N100m Cikin Kudin Sata

Dariye ya kuma bayyana cewa hukunta shi da aka yi tare da tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame, kan aikata rashawa bai kawo karshen sama da fadi da ake yi kan dukiyar kasar ba.

Dariye
Tsohon Gwamnan Arewa Da Buhari Ya Yi Wa Afuwa Ya Fadi Yadda Za'a Kawo Karshen Cin Hanci da Rashawa a Najeriya Hoto: Premium Times
Asali: Depositphotos

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“An daure Dariye da Nyame a magarkama. Shin ya kawo karshen cin hanci da rashawa? Kamar yadda na fada ma mai shariana, kana da damar daure ni har na tsawon shekaru 200, idan har hakan zai kawo karshen cin hanci da rashawa, zan yi godiya ga Allah.”

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa Dariye, wanda aka hukunta kan sace naira biliyan 1.16 yayin da yake matsayin gwamnan jihar Plateau daga 1999 zuwa 2007, afuwa a ranar 14 ga watan Afrilun 2022.

An yi masa afuwa ne tare da Nyame, wanda aka hukunta shi shima kan satar naira biliyan 1.6 an kuma sake su daga kurkukun Kuje a ranar 8 ga watan Agustan 2022.

Kara karanta wannan

Bidiyo: 'Yar Najeriya ta mutu yayin da ake mata tiyatar cikon mazaunai a India

Sai dai kuma, Dariye, wanda yayi godiya ga shugaban kasar kan afuwar da yayi masu, ya ce akwai siyasa a lamarin garkame shi da aka yi, yana mai cewa wasu sun yi abun da ya fi nasa muni amma aka yafe masu.

Da aka tambaye shi game da yadda za a kawo karshen rashawa a kasar, Dariye ya ce:

“Idan muna son kawo karshen cin hanci da rashawa, ba abu ne na rana daya ba; za ka dauki rashawa don magance rashawa. Kuma idan ka fara isar da manufofi, bara na baka misali: idan tashar jirgin kasa na aiki, ba tare da wadannan mutane sun yi zagon kasa ba, zai rage wahala sosai kan mutanenmu, zai rage farashin kayayyaki, kayan gona.
“Abubuwa basa tafiya, wasu mutane da cin gajiyar lamarin, suna wahalar da matakan gwamnati.”

Tsohon sanatan na yankin Plateau ta tsakiya ya kuma bayyana cewa ba zai nemi kowace kujerar gwamnati ba a 2023, rahoton Pulse.ng.

Kara karanta wannan

EFCC ba za su iya yakar rashawa ba a Najeriya, dan takarar shugaban kasa ya fadi dalili

Ya kara da cewa:

“Bana neman takara a wannan karon, zan dauki hutu.”

Sanatan Kano Ya Bayyana Ainahin Wanda Osinbajo Yake Goyon Baya A Zaben Shugaban Kasa Na 2023

A wani labari na daban, Sanata Kabiru Gaya ya tabbatar da cewar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo suna aiki kai da fata.

Sanatan ya ce bayan Tinubu ya bayyana a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki, ya ziyarci Osinbajo a gidansa sannan ya nemi ya goya masa baya.

Daily Trust ta rahoto cewa Sanata Gaya ya kara da cewa sabanin rade-radin da ke yawo, ba a matar da mataimakin shugaban kasar saniyar ware ba a wajen kafa tawagar yakin neman zaben takarar shugabancin APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng