Babban Sarki A Najeriya Ya Yi Hannun Riga Da Matarsa Kan Tikitin Takarar Mataimakiyar Gwamna

Babban Sarki A Najeriya Ya Yi Hannun Riga Da Matarsa Kan Tikitin Takarar Mataimakiyar Gwamna

  • Oba Kamoroudeen Animashaun, Olaja na Epe a Jihar Legas ya nesanta kansa da takarar mataimakiyar gwamna da matarsa Olori Morenike Abeni ke yi
  • Oba Animashaun ya bayyana cewa Olori Morenike ba ta sanar da shi ba kuma bata nemi shawararsa ba kafin shiga siyasar
  • Basaraken na Epe ya yi kira ga dukkan mabiyansa, abokansa da na kusa da shi kiyayi Olori Morenike bisa siyasar da ta ke yi yana mai cewa babu hannunsa

Legas - Oloja na Epe, Oba Kamoroudeen Animashaun, ya nesanta kansa daga takarar mataimakiyar gwamna da matarsa, Olori Morenike Abeni Animashaun ke yi a karkashin jam'iyyar Social Democratic Party, SDP.

A cikin sanarwar da ya fitar a Legas, sarkin ya ce matarsa ba ta sanar da shi cewa za ta shiga takarar siyasa ba kuma ba ta nemi izininsa ba, The Nation News ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Ban Taba Satar Ko Sisi Ba, Daidai Da Naira 10, In Ji Dan Takarar Shugaban Kasa Daga Arewacin Najeriya

Oba Kamoroudeen Animashaun
Babban Sarki A Najeriya Ya Yi Hannun Riga Da Matarsa Kan Tikitin Takarar Mataimakiyar Gwamna. Hoto: The Nation News.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanarwar ta ce:

"An janyo hankali na kan harkokin siyasa da Olori Morenike Abeni Animashaun ta shiga a baya-bayan nan, musamman shiga jam'iyyar SDP. Ina son sanar da cewa ba ta taba tattauna abin da ni ba cewa za ta nemi kujerar mataimakiyar gwamna kuma ban bata izinin neman kujerar siyasa ba tunda farko."

Oba Animashaun ya ce kasancewarsa mamba na majalisar sarakuna na Legas, ana tsammaninsa ya tallafawa gwamnati mai ci ne wurin isar da romon demokradiyya ga mutanensa a maimakon shiga siyasan jam'iyya.

Oba Animashaun ya yi kira ga mabiyansa da na kusa da shi su kiyayi Olori Morenike Abeni

Ya yi kira ga mabiyansa, abokansa da sauran na kusa da shi su yi taka tsantsan wurin harka da Olori bisa duk wani abu da ya shafi siyasarta, yana mai cewa babu hannunsa ciki.

Kara karanta wannan

Su suka bata Najeriya: Tinubu ya caccaki Atiku, ya ce PDP ba za ta lashe zaben 2023 ba

"Ba matsala bane a yi wa Olori Morenike Abeni fatan alheri a wannan siyasar da ta shiga ba tare da neman shawara ba a yayin da na ke fatan za ta janye nan ba da dadewa ba, ko da domin daraja ta na basaraken gargadiya da ake girmamawa."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164