Saura Kiris a Yi Sallama da Batun Yajin Aikin ASUU, Inji Kakakin Majalisar Wakilai

Saura Kiris a Yi Sallama da Batun Yajin Aikin ASUU, Inji Kakakin Majalisar Wakilai

  • Kakakin majalisar wakilai ya bayyana kwarin gwiwar cewa, kungiyar ASUU za koma bakin aiki nan ba da dadewa ba
  • Kungiyar ASUU ta yabawa majalisar wakilai bisa tsoma baki da kuma samar da mafita ga kungiyar
  • Kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki tun watan Fabrairun bana, dalibai sun shafe watanni sama bakwai a kasa

FCT, Abuja - Kakakin majalisar wakilai ta kasa, Femi Gbajabiamila ya tabbatarwa 'yan Najeriya cewa, nan kusa kadan kungiyar malaman jami'a za ta koma bakin aiki, The Nation ta ruwaito.

Kakakin na majalisa ya bayyana hakan ne a ganawarsa da shugaban ASUU, Fafesa Emmanuel Osodeke da sauran kusoshin kungiyar da yammacin yau Litinin 10 ga watan Oktoba.

Majalisa ta shawo kan ASUU, za a bude jami'o'i
Saura kiris a yi sallama da batun yajin aikin ASUU, inji shugaban majalisar wakilai | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Shugaban ASUU ya ce, da tun farko majalisar wakilai ta shiga lamarin ASUU da gwamnatin Buhari, da cikin kwanaki za a warware duk wata matsala tare da janye yajin aikin.

Kara karanta wannan

2015: Daga neman canji, 'yan Najeriya suka zabi Buhari; yunwa, fatara da rashin tsaro

Hakazalika, kungiyar ta ASUU ta kuma bayyana godiya da yabo ga majalisar wakilai bisa tsoma baki tare da kawo mafita ga yajin aiki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Vanguard ta ruwaito shugaban ASUU na karawa da cewa:

"A karon farko, mun ga haske a karshen lamarin."

Nan da Kwanaki Kadan Za a Janye Yajin Aikin ASUU, Lauyan ASUU Falana Ya Magantu

A wani labarin, babban lauya Femi Falana ya bayyana kwarin gwiwar cewa, nan ba da dadewa kungiyar malaman jami'a karkashin ASUU za su janye yajin aikin da suke yi tun watan Fabrairun bana.

Falana ya bayyana cewa, janye yajin aikin ba wai makwanni zai dauka ba, zai zo ne cikin 'yan kwanaki masu zuwa nan kusa, rahoton Tribune Nigeria.

Babban lauyan ya bayyana hakan ne a yau Litinin 10 ga watan Oktoba a jihar Legas yayin bikin kaddamar da littafi mai suna Breaking Coconut With Your Head da Lanre Arogundade ya wallafa.

Kara karanta wannan

Su suka bata Najeriya: Tinubu ya caccaki Atiku, ya ce PDP ba za ta lashe zaben 2023 ba

Ya kuma bayyana cewa, akwai yiwuwar dinke duk wata baraka ta yajin aikin a wajen kotu, kamar yadda aka ba kungiyar shawari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.