Mata da ‘Yan Yara 30 Sun Yi Shahada, Sun Nutse a Ruwa Za Su Tserewa ‘Yan Bindiga
- ‘Yan kananan yara da mata sun hallaka yayin tserewa ‘yan bindiga a wani kauyen Zamfara
- Mutanen Birnin Waje a karamar hukumar Bukkuyum sun tashi da harbe-harben bindigogi da asuba
- Jama’a sun nemi su tserewa ‘yan bindigan, amma sai wasunsu suka gamu da hadarin jirgin ruwa
Zamfara - Fiye da mutane 30 suka hallaka kwanakin baya a lokacin da suke neman kubuta daga wasu miyagun ‘yan bindiga a kauyen Zamfara.
Jaridar nan ta Vanguard ta rahoto cewa kananan yara da mata da neman tsira da rayuwarsu sun gamu da ajalinsu a tsakiyar makon da ya gabata.
Abin ya faru ne yayin da kwale-kwalen da ya dauko wadannan mutane ya nutse a cikin ruwa. Ana zargin mutane kusan 30 ne suka yi shahada.
Mazauna garin Birnin Waje a garin Bukkuyum na jihar Zamfara sun ce ‘yan bindiga sun auko masu da kimanin karfe 6:00 na safiyar ranar Laraba.
Premium Times tace Birnin Waje kauye da ke kusa da ruwa da ke kilomita biyu da Bukkuyum. Wani hadimin gwamna ya tabbatar da haka a shafinsa.
Ibrahim Zauma ya yi magana a Facebook, yace hadarin jirgin ruwa ya kashe yara da mata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga da Assalatu
Wani mazaunin yankin ya shaidawa manema labarai cewa ana shirin sallar asuba sai ‘yan bindiga suka shigo masu gari, suka fara harbe-harbe ta ko ina.
‘Yan ta’addan sun shigo garin ta kofar yamma, kafin ta’adinsu ya yi nisa sai sauran mutanen da suka farga suka fara yunkurin tserewa zuwa Zauma.
Kafin a kai kauyen Zauma, dole sai an tsallaka wani rafi. A dalilin haka kananan yara da mata da-dama suka shiga cikin kwale-kwale domin su tsira.
Da aka tuntube shi, wani Lawali Sambo ya bayyana cewa ana kokarin dauko gawawwakin wadanda suka kife a jiragen, suka nutse a cikin ruwa.
Har zuwa lokacin da aka zanta da Sambo, ‘yan ta’addan suna cikin Birnin Waje. Ana zargin miyagun sun kwana a garin ne, suka fara ta’adi da asuba.
Aikin jirgin kasan Kaduna
A yau ne aka ji labari bayan shekaru bakwai da rabi a mulki, Gwamnatin Najeriya ta fito ta yi bayanin dalilin rashin ƙarasa layin dogon Kaduna-Kano.
Gwamnatin Muhammadu Buhari ta tsara kammala waɗannan ayyuka na layin dogo ne kafin ƙarewar wa’adin mulkin nan, yanzu saura 'yan watanni.
Asali: Legit.ng