Shirin BBNaija Wakili Ne Na Shaidan a Doron Kasa, Inji Kungiyar MURIC
- Kungiyar hare hakkin musulmai ta MURIC ta bayyana goyon bayanta ga kawo karshen shirin da tace na yada tsiraici ne; BBNaija
- A lokuta da dama kungiyar ta sha bayyana rashin amincewarta da shirin mai nuna abubuwan da basu dace da tarbiyya ba inji MURIC
- MURIC ta koka da yadda wani gwamna ya kwashi gida da kudade ya ba wanda ya lashe wasan BBNaija
Najeriya - Kungiyar kare hakkin musulmai ta MURIC ta goyi bayan batun Segun Runsewe na cewa majalisar dokokin kasa ta ba hukumar al'adu ta kasa (NCAC) ikon ji da lamarin BBNaija domin dakile yaduwar tsiraici.
Wannan batu na goyon baya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ya fitar a yau Lahadi 9 ga watan Oktoba.
Darakta janar na NCAC ya bukaci majalisar dokokin kasar nan da ta ba hukumarsa damar tunkarar shirin BBNaija don dakile yaduwar tsiraici a kasar.
Segun ya bayyana hakan ne a ranar 4 ga watan Oktoba, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar MURIC, tana goyon bayan Segun, kuma tabbas shirin BBNaija ba komai bane face kafar yada barna kuma wakilin shaidan.
Mun sha kira a kawo karshen BBNaija
Hakazalika, MURIC ta bayyana cewa, a baya ta sha kira ga gwamnati da ta kawo karshen shirin ganin cewa ya saba da tarbiyya da addini.
A bangare guda, ta ce kullum tana Allah wadai da shirin tare da nuna kyamarsa.
MURIC ta kuma tuna da cewa, akwai lokacin da wani gwamna a kasar nan ya dauki gida sukutum da guda da tsabar kudi N5m ya ba wanda ya lashe gasar da shirin na BBNaija ke gudanarwa.
Daga karshe, daraktan MURIC ya ce ya fahimci a kasar nan babu dokar da ta hana nuna tsiraici a talabijin, don haka lokaci ya yi da ya kamata a samar da irin wadannan dokokin.
Don girman Allah a dakatar da shirin BBNaija - Malamin coci ya roki FG
A wani labarin, Ifeanyi Akunna, babban malamin cocin Epiphany da ke Abuja ya roki gwamnatin tarayya da ta dakatar da shirin Big Brother Nigeria (BBNaija) da sauran shirye shirye makamantansa.
BBNaija wani shiri ne da ake gabatarwa na rayuwar zahiri, inda mutanen cikin shirin ke killace a gida daya na tsawon wani lokaci, kuma ana bayar da kyautar makudan kudade.
Akunna ya yi wannan kiran a cikin wani sako da ya yi wa take: "Gidan da aka bude shi don alfasha', sakon da ya rabawa manema labarai a ranar Alhamis a Abuja.
Asali: Legit.ng