'Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Gunduma da Wasu Mutum Uku a Jihar Filato

'Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Gunduma da Wasu Mutum Uku a Jihar Filato

  • 'Yan bindiga sun kashe Mai Anguwa da wasu mutum uku a wani sabon hari da suka kai yankin ƙaramar hukumar Bokkos a Filato
  • Bayanai sun nuna cewa maharan sun shiga ƙauyen Kulias (Mabel) suka buɗe wa mutane wuta kan mai uwa da wabi
  • Da aka nemi jin ta bakin kakakin hukumar yan sanda reshen Filato, DSP Alabo, bai ɗaga kiran ba kuma bai turo amsar sakonni ba

Plateau - Wasu miyagu da ake zaton 'yan bindiga ne sun kashe shugaban gunduma da wasu mutum uku a yankin Kulias (Mabel) dake Batura, ƙaramar hukumar Bokkos jihar Filato.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa yankin na fama da yawan hare-haren 'yan bindiga, wanda a wannan karon ya yi ajalin mutum huɗu, wasu da yawa suka jikkata.

Taswirar jihar Filato.
'Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Gunduma da Wasu Mutum Uku a Jihar Filato Hoto: thenation
Asali: UGC

AIT Live ta ruwaito cewa maharan sun kaddamar da mummunan nufinsu ne ranar Asabar da misalin ƙarfe 11:00 na dare lokacin mafi yawan mutane sun kwanta bacci.

Kara karanta wannan

Hankula Sun Tashi Yayin Da Aka Nemi Mutum 30 Aka Rasa Sakamakon Kifewar Kwale-Kwale A Wata Jihar Najeriya

Daga cikin waɗanda aka tabbatar da sun rasa rayukansu sanadin harin har da Mai Anguwa (Watau Shugaban Ƙauyen) da wasu mutum uku.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tsohon Kansilan gundumar Batura da ke ƙaramar hukumar Bokkos, Honorabul Josiah Mahwash, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai.

Yace yan bindiga da adadi mai yawa sun shiga ƙauyen inda suka shafe 'yan mintoci wajen aikata nufinsu, sannan suka fice.

Wani da ya yi ikirarin cewa shi mazaunin yankin ne, Rafan Dafang James, yace yan bindigan sun shiga ƙauyen na jihar Filato, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda reshen jihar Filato, DSP Alfred Alabo, bai ɗaga kiran wayar salulan da aka masa ba ko turo amsoshin sakonnin da aka aike masa ba domin jin ta bakin hukumarsu.

Yan bindiga sun kashe shugaban matasan APC

Kara karanta wannan

An damke Soja yana baiwa masu garkuwa da mutane hayar bindiga AK-47

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Halaka Shugaban Matasan Jam'iyyar APC a Jihar Enugu

Tsagerun 'yan bindiga sun bindige Hon. Lucky Okechukwu, shugaban matasan jam’iyyar APC a karamar hukumar Igboeze ta kudu da ke jihar Enugu.

An tattaro cewa maharan sun farmaki marigayin ne a daren ranar Asabar, 8 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262