Yadda 'Dan Sanda ya Manna Min Sharri, Ya Tatse N100k daga Wurina, Matashi

Yadda 'Dan Sanda ya Manna Min Sharri, Ya Tatse N100k daga Wurina, Matashi

  • Wani mutum mai suna Oluwagbadura ya shaida wa duniya yadda ta kaya tsakaninsa da wasu ‘yan sanda shida a shafinsa na Twitter
  • A cewarsa, bayan tsayar da shi inda su ka bincike shi ba tare da gano wani abu tartare da shi na laifi ba, sai da su ka tilasta masa amsa laifuka
  • Ya ce bayan kin amincewa ya amsa laifin ne su ka tasa keyarsa har wurin mai POS inda su ka kwashi N100,000 daga asusunsa ba banki

Legas - Wani mutum mai suna Oluwagbadura ya bayyana yadda ya kwashi hannunsa a hannunn wasu ‘yan sanda wadanda su ka tatse shi tas a Soliki, wuraren Aguda cikin Jihar Legas, inda su ka tilasta masa fitowa da N100,000.

Mutumin ya ce ‘yan sanda shida ne su ka dakatar da shi da misalin karfe 1:45 na ranar Alhamis, inda su ka bincikesa sannan su ka amshi wayarsa don dubata itama. Bayan sun duba, babu abu na rashin gaskiya da su ka gani.

Oluwagbadura ya shaida yadda su ka kira shi da mai laifi bayan ganin wata tattaunawar da yayi da abokinsa ta WhatsApp, hakan yasa su ka tilasta masa bin su ofishin ‘yan sanda.

Ya shaida yadda ta kaya masa tsakaninsa da ‘yan sandan ta shafinsa na Twitter, @ojogbadura, tare da bayani dalla-dalla akan yadda ‘yan sandan su ka yi yunkurin harbinsa lokacin da ya musanta zarginsu.

Kamar yadda ya wallafa:

“Rundunar ‘Yan sanda Najeriya yau (6 ga watan Oktoban 2022) da misalin karfe 3:44 na rana su ka raka ni har wurin mai POS inda su ka cire N100,000 daga kudaden da na sha wahalar tarawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Da misalin karfe 1:45 ne ‘yan sandan Najeriya su ka dakatar da ni a Soliki Aguda, cikin Jihar Legas sannan su ka bincikeni tas ba tare da ganin wani abu na rashin gaskiya ba.

“Sun bincike wayata sosai. Sai su ka fara kirana da mara gaskiya bayan tattaunawa da abokaina ta WhatsApp. Sun yi yunkurin harbin da kuma rufe ni!
“Daga nan ne su ka zarce dani ofishinsu, wanda ba ya da nisa da wurin, inda su ka tilasta ni da in amsa cewa ba na da gaskiya. Na ki amincewa da hakan.”

Oluwagbadura ya ci gaba da bayyana yadda su ka umarceshi da ya rubuta takardar daga nan su ka bukaci N100,000 daga wurinsa a matsayin kudin beli. Anan ne ya wallafa hoton shaidar biyansu kudin.

Ya bayyana sunayensu inda yace akwai Abdulkareem Sulaiman, Ojo ozeigbe, wanda shi ne wanda yace zai iya cutar da shi kuma babu abinda zai faru. Sauran kuma duk mufti ne wadanda su ka goyi bayan sauran.

Ya ce yana bukatar adalci sannan a dawo masa da kudadensa.

Daga bisani Oluwagbadura ya bayyana cewa an biya shi kudinsa. Ya mike godiyarsa ga @SavvyRinu, @BenHundeyin, @segalink da kuma DPO.

Yan Sanda Sun Sha Alwashin Tsamo Jami’ar da ta Rikewa Matar Atiku Jaka

A wani labari na daban, rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF) tana shirin daukar mummunan mataki akan jami’arsu da ke rike wa Titi, matar dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP jaka, jaridar The Cable ta rahoto.

Dan takarar shugaban kasar a ranar Laraba ya wallafa wasu hotunan matarsa a Twitter a wani taro da suka yi a Abuja.

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa:

“Taron S.H.E initiative daga matata, Hajia Titi Atiku Abubakar, ya kunshi abubuwa da dama da nafi so. Akwai harkar tsaro, lafiya da ilimi. Wadannan abubuwan guda uku su ne ke bai wa ko wanne mutum ‘yanci, musamman yara mata.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel