Ba Zan Sake Shiga Yarjejejiya da ASUU Ba, Shugaba Buhari Ya Magantu
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana gaskiyar abin da ya kudurta game da kungiyar malaman jami'a ASUU
- Shugaban yace ba zai sake shiga yarjejeniyar da ba zai iya cikawa ba a yanzu saboda wasu dalilai da ya gani
- ASUU ta shafe watanni sama da bakwai tana yajin aikin neman hakkinta a hannun gwamnatin tarayya
FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya ya yiwa kungiyoyin jami'o'in kasar bayani, ya ce ba zai yi musu alkawarin da ba zai iya cikawa ba.
Shugaban ya bayyana hakan ne a martaninsa ga kungiyar malaman jami'a ta ASUU dake yajin aiki tun watan Fabrairun bana, Daily Trust ta ruwaito.
Sai dai, shugaban ya ce gwamnati na rike da alkawuran da ta dauka kuma ta rubuta yarjejeniya da ASUU a baya.
Buhari ya ce, a yanzu dai gwamnati kadai ba za ta iya daukar nauyin dukkan bukatun jami'o'in kasar nan ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya bayyana cewa, fannin ilimi a kasar nan ta kamata ya zama nauyi ne dake kan al'umma da kuma gwamnatin kanta.
Kokarin da gwamnati ke yi a fannin jin dadin malamai
Hakazalika, ya yi karin haske da cewa, gwamnatinsa ta ware N470.0bn domin habakawa da inganta fannin albashi da jin dadin malamai a kasar nan.
Hakazalika, ya koka kan yadda har yanzu jami'o'in Najeriya ke garkame saboda rashin fahimtar juna tsakanin gwamnatinsa da kungiyar malaman ta ASUU.
Idan baku manta ba, a yau din ne dai kotun daukaka kara ta umarci kungiyar malaman jami'a da ta gaggauta janye yajin aikin da take yi, haka nan This Day ta ruwaito.
A baya kotun ma'aikata ta umarci ASUU ta janey yajin aiki, amma hakan bai yiwu ba saboda kungiyar ta daukaka kara.
Mataki gaba dai shine tafiya kotun koli matukar ASUU ta shirya, amma har zuwa yanzu dai kungiyar bata yi martani ko bayyana komawa aikin ba.
Kungiyar ASUU Ta Maka Gwamnatin Tarayya a Kotu Saboda Yiwa Kishiyoyinta Rajista
A wani labarin, kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) za ta tunkari kotun ma'aikata kan lamarin da gwamnati ta gabatar na yiwa kungiyoyin dake kishiyantarta rajista.
Lauyan ASUU, Femi Falana ne ya shaidawa Channels Tv cewa, kungiyar za ta tunkari kotun ma'aikata domin kai kokenta.
Hakazalika, shugaban kungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke ya tabbatar da hakan a wata tattaunawa da aka yi dashi a ranar Alhamis 6 ga watan Okotoba.
Asali: Legit.ng