Hukumar Kula Da Ayyukan Yan Sanda Ta Yi Wa DCP Guda 40 Da Wasu Karin Girma, Ta Fitar Da Sunayensu

Hukumar Kula Da Ayyukan Yan Sanda Ta Yi Wa DCP Guda 40 Da Wasu Karin Girma, Ta Fitar Da Sunayensu

  • Hukumar kula da ayyukan yan sanda, PSC, ta yi wa wasu jami'ai masu mukamin DCP karin girma zuwa kwamishinoni.
  • Rundunar yan sandan ta yi kira ga wadanda aka yi wa karin girman su kara zage damtse wurin aiki da yi wa Najeriya hidima
  • PSC ta kuma yi wa jami'an yan sandan Najeriya alkawarin za ta tabbatar ana yi musu karin girma ba jinkiri idan sun cancanta

Abuja - Hukumar kula da ayyukan yan sanda, PSC, ta amince da yi wa mataimakan kwamishina 40 arin girma zuwa kwamishina.

Hukumar ta kuma amince da yi wa mataimakan kwamishina saboda gurbin da ba a cike ba a bangaren kiwon lafiya.

An yi wa sabbin kwamishinonin karin girman ne bayan tattaunawa/tambayoyi da aka musu a gaban kwamitin da Mai shari'a Clara Bata Ogunbiyi JSC (mai murabus) ta jagoranta.

Kara karanta wannan

Yadda Hadimin Gumi ya Dinga Tarwatsa Kokarin FG na Ceto Fasinjojin Jirgin Kasa, Jami’i

Usman Baba
PSC Ta Yi Wa DCP Guda 40 Da Wasu Karin Girma. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na cikin wani sanarwa ce da shugaban sashin watsa labarai na PSC, Ikechukwu Ani, ya fitar a ranar Juma'a, The Punch ta rahoto.

A cewar sanarwar, hukumar ta kuma amince da yi wa CP Abdul Yari Lafia da CP Rudouf Echebi karin girma zuwa mukamin mataimakan sifeta janar.

Sunayen wadanda aka yi wa karin girma

Sabbin kwamishinonin yan sandan da aka yi wa karin girma sune:

  • Adebola Ayinde Hamzat, yanzu DCP, SCID, Jihar Ondo
  • Idegwu Basil Okuoma, DCP Federal Operations, Hedkwatar Yan Sanda Abuja
  • Zachariah Dera Achinyan, National Defence College Abuja
  • Sule Balarebe, DCP DFA, Rundunar yan sandan Jihar Sokoto
  • Zango Ibrahim Baba, DCP SFU, FCIID Annex, Legas
  • Maiyaki Mohammed Baba, DCP Admin, Rundunar Jihar Kebbi
  • Ishiaku Mohammed, DCP Bangaren Kudi, Hedkwatar Yan Sanda
  • Margret Agebe Ochalla, Jagora Tawaga, Sashin Sa Ido na IGP kuma a yanzu shugaban sashin kula da batutuwan da suka shafi jinsi na rundunar yan sanda.
  • Benneth Igwe, DCP OPs Rundunar Abuja da
  • Mohammed Abdul Suleiman, na biyu, Jami'in Ilmantarwa na rundunar.

Kara karanta wannan

Abokin Takarar Atiku Abubakar a PDP Ya Samu Mukami a Kwamitin Neman Zabensa

Saura sun hada da:

  • Ajala Elijah Ayoola, DCP FMIU, Lagos
  • Romokere God’s Gift Ibani, DCP SCID, Rundunar Jihar Abia
  • Akika Augustine, Mataimakin Kwamanda, Kwalejin Yan Sanda, Ikeja
  • Peter W. wagbara, DCP Admin, Rundunar Jihar Rivers;
  • Ogundare Dare Emmanuel, DCP SCID, Rundunar Jihar Kebbi
  • Chris Omonzokpea Aimionowane, DCP Ops Zone 13 Ukpo
  • Augustina Nwuka Ogbodo, former DCP Admin, FCT kuma yanzu a FCIID, Abuja;
  • Polycarp Chilaka Dibia, DCP Zone 6 Benin
  • Ogunrinde Banji, DCP Force CID, Annex Lagos
  • Sybil Olufunmilayo Akinfenwa, DCP Homic*de, FCIID Annex Lagos
  • Ita Lazarus Uko-Udom DCP DFA Zone 12 Bauchi
  • Samuel Titus Musa, DCP SCID, Rundunar Jihar Enugu
  • Ochogwu Abbas Ogbeh, na biyu, bangaren shari'a

Sai kuma:

  • John Ayuba Babangida, DCP DFA, Rundunar Jihar Ekiti
  • Kayode Adetunmbi, DCP Ops, Zone 9 Umuahia
  • Aderemi Olufemi Adeoye, DCP OPs Anambra State Command;
  • Dayo Ariyo, DCP Boarder Patrol;
  • Stephen Olarewaju, DCP, DFA, Rundunar Jihar Nasarawa
  • Remigius Okwor, DCP, DCP Force Headquarters Police Accounts and Budget Annex Lagos
  • Kenechukwu Onwuemelie, DCP SCID, Rundunar Jihar Ogun
  • Fayodade Adegoke Mustapha, DCP SCID Rundunar Jihar Lagos
  • Adegboyega Funsho Adegboye, DCP OPs Rundunar Jihar Ondo
  • Umar Shehu Nadada, DCP OPs Rundunar Jihar Nasarawa
  • Mustapha Mohammed Bala, DCP SCID Rundunar Jihar Imo
  • Taiwo Olatunde Adeleke, DCP OPs PAP Western Command Lagos
  • Ibrahim Abdullahi, DCP General Investigation FIICD; Akinwale Adeniran, DCP DFA, Zone 8 Lokoja
  • Mamman Dauda, DCP OPs Rundunar Jihar Zamfara
  • Mohammed Bala Labbo, DCP Sadarwa, Rundunar Jihar Kebbi
  • Umaru Madaki, DCP Bangaren Aikin Jinya, Rundunar Jihar Kano
  • Nkechi Eze, O/C Bangaren Lafiya Rundunar Jihar Rivers
  • Garba Emmanuel Nzukwen, O/C Medical, Rundunar Jihar

Kara karanta wannan

Yadda na kwashe shekaru da dama ina jinyar mijina kan ciwon PTSD, Aisha Buhari

Shugaban PSC ta bukaci wadanda aka yi wa karin girman su kara kaimi da zage damtse wurin aiki

Shugaban wucin gadi na hukumar ta yi kira ga wadanda aka yi wa karin girman su sake kara kaimi wurin aiki da yi wa kasarsu hidima.

Mai shari'a Ogunbiyi ta ce hukumar za ta cigaba da tabbatar da ganin ba a jinkirin yi wa yan sandan karin girma, tare da adalci bisa girma da guraben da akwai.

Kano: Hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta kara wa 'yan sanda 252 girma

Habu Ahmad, kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, ya yi kira ga 'yan sanda 252 da aka kara wa girma da su nuna kwarewa tare da mayar da hankali wurin sauke nauyin da aka dora musu.

Ahmad ya sanar da hakan ne a wata takarda da ta fita ta hannun kakakin rundunar 'yan sandan a ranar Laraba, 29 ga watan Yuli, a jihar Kano, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel