Kano: Hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta kara wa 'yan sanda 252 girma
- Hukumar 'yan sanda a jihar Kano ta kara wa jami'an 'yan sanda 252 girma
- Kwamishinan 'yan sandan jihar, Habu Ahmad ya yi kira garesu da su nuna kwarewa tare da mayar da hankali wurin sauke nauyin da aka dora musu
- Ahmad ya yi kira ga jama'ar jihar da su kiyaye dokokin dakile yaduwar cutar coronavirus
- Ya kuma yi wa Musulmai fatan yin bikin Sallah cikin lumana
Habu Ahmad, kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, ya yi kira ga 'yan sanda 252 da aka kara wa girma da su nuna kwarewa tare da mayar da hankali wurin sauke nauyin da aka dora musu.
Ahmad ya sanar da hakan ne a wata takarda da ta fita ta hannun kakakin rundunar 'yan sandan a ranar Laraba, 29 ga watan Yuli, a jihar Kano, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Takardar ta ce kwamishinan 'yan sandan ya sanar da hakan ne yayin bikin karin girma ga 'yan sandan a ranar Talata.
Ahmad ya taya 'yan sandan murna da karin girman da suka samu.
Ya ce: "Ga duk wanda aka daura wa nauyi, ana tsammanin zai iya saukesa.”
Ya kuma jaddada cewa akwai bukatar manyan 'yan sandan su jajirce wurin sauke nauyin da ke kansu kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
KU KARANTA KUMA: Barazanar harin 'Yan Bindiga a Kano: Rundunar Yan sanda ta yi ƙarin haske
A yayin kira ga jama'ar jihar da su kiyaye dokokin dakile yaduwar cutar coronavirus, Ahmad ya yi wa Musulmin jihar fatan yin bikin sallah babba cikin lumana.
Daya daga cikin 'yan sanda da aka kara wa girma, SP Mukhtar Sabiu, ya yabawa IGP Mohammed Adamu da hukumar 'yan sanda a kan karamcin da suka yi musu.
Sabiu ya dauki alkawarin mayar da hankali tare da jajircewa a kan aikinsa.
Kamar yadda takardar tace, an kara wa 'yan sanda masu mukamin SP 9, DSP 4 da ASP 239 girma.
Takardar ta kara da cewa a cikin wadanda suka samu halartar bikin akwai Birgediya janar B.A Alabi, Alhassan N. Mohammed, shugaban hukumar jami'an tsaro na farin kaya, Air Commodore Mohammed Isah da Abu Audu, babban kwamandan NSCDC.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng