Shehu Sani: An Sace Wayar Namadi Sambo A Wurin Kaddamar Da Littafi A Abuja
- An sace wayar salular tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Arc Namadi Sambo a babban birnin tarayya Abuja
- Tsohon sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya ce lamarin ya faru ne wurin kaddamar da littafi kan marigayi Gwamna Solomon Lar
- Sani ya ce akwai jami'an tsaro matuka a wurin taron amma abin mamaki duk da hakan aka samu wani ya ratsa ya sace wayar tsohon gwamnan na Kaduna
FCT, Abuja - An sace wayar salular tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Arc. Namadi Sambo a wurin wani taro a babban birnin tarayya, Abuja.
Sanata Shehu, tsohon dan majalisar tarayya, wanda ya bayyana hakan a Twitter a ranar Alhamis, ya ce lamarin ya faru ne a wurin kaddamar da littafin "Chronicles Of The Rainbow", tarihin marigayi Gwamna Solomon Lar.
Ya ce akwai jami'an tsaro sosai a wurin taron amma wani ya 'kutsa' ya sace wayar salulan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya rubuta:
"Abin mamaki ne yadda wani ya tsallake matakan tsaro ya sace wayar tsohon mataimakin shugaban kasa Sambo a taron kaddamar da litafin marigayi Gwamna Solomon Lar a Abuja."
Sambo ne mataimakin shugaban kasar Najeriya daga ranar 19 ga watan Mayun 2010 zuwa 29 ga watan Mayun 2015.
Ya yi gwamna a jihar Kaduna daga 2007 zuwa 2010.
Na yi farin cikin ganin an girmama mahaifi na - Beni Lar
Yayin da ta ke magana da manema labarai, yar Lar, wacce yar majalisar wakilai na tarayya ne, Hon. Beni Lar ta ce:
"Na yi farin cikin ganin an karrama mahaifi na. Ina farin cikin cewa bayan shekaru da ya yi wa Najeriya hidima, ya mutu ba tare da mallakar gida a Abuja ba, wani karamin gida kawai gare shi a Jos. Ya yi wa mutane hidima da dukkan abin da ya ke da shi kuma na ji dadin yadda kowa a kasar nan."
Atiku Ya Fi Kowane Ɗan Takara Cancanta Ya Zama Shugaban Kasa a 2023, Namadi Sambo
wani rahoton, tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, ya bayyana Atiku Abubakar, mai neman zama shugaban kasa a inuwar PDP, a matsayin wanda ya fi dacewa da Najeriya a 2023.
Premium Times tace Sambo ya faɗi haka ne a Abuja a wurin taron gabatar da Litattafai kan Atiku da kaddamar da tawagar yaƙim neman zaɓen PDP.
A cewarsa, ba ko shakka Atiku ne mutumin da zai iya baje matsalolin Najeriya a faifai kuma yake da kwarewar lalubo hanyar warware su baki ɗaya.
Asali: Legit.ng