Gwamnati ta biya ma yan matan chibok kudin makaranta, miliyan 165

Gwamnati ta biya ma yan matan chibok kudin makaranta, miliyan 165

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a biya kimanin naira miliyan 164,763,759 a matsayin kudin makarantar da suke yi, su dari da shida, 106, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan matan na karatu ne a Jami’ar Amurka dake Najeriya, a jihar Yola, kamar yadda Kaakakin shugaban kasa, Garba Shehu ya bayyana, inda yace a yanzu haka Buhari na sake nazari akan walwalan yan matan.

KU KARANTA: Kin zuwa Kano: Wasu mafusata sun cire katon hoton Shugaba Buhari a jihar Kano

Garba ya bayyana cewa shugaba Buhari ya jajirce wajen ganin an ceto kafatanin yan matan na chibok, wadanda Boko Haram suka yi garkuwa da su, sa’annan ya yaba da cigaban da aka samu dangane da mata 106 da aka kwato.

Gwamnati ta biya ma yan matan chibok kudin makaranta, miliyan 165
Chibok

Shehu yace zaman yaran a makarantar wani sabon shafi ne a rayuwarsu, inda ya jaddada manufar shugaba Buhari na ganin sun samu ilimi ingantacce, har su kammala karatunsu a jami’a.

Sai dai kafin garzayawa dasu jami’ar, sai da aka killace su a cibiyar cigaban mata na tsawon wata tara, tun daga watan Janairun 2017, zuwa Satumbar 2017, inda ake basu darasi akan Turanci, Lissafi, ilimin halitta, ilimin noma da kuma ilimin zama dan kasa na gari.

Haka zalika an horar dasu ayyukan hannu, tare da gayyato kwararru da zasu taimaka wajen rage musu fargaba, tare da gayyto Malaman addini don su yi musu wa’azi, duk da haka akwai likitoci guda biyu jibge a gidan da suke, sa’anann iyayensu na samun daman ziyartar su.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng