Da Duminsa: ‘Yan Ta’adda Sun Sako Sauran Fasinjoji 23 na Harin Jirgin Kasan Abj-Kd

Da Duminsa: ‘Yan Ta’adda Sun Sako Sauran Fasinjoji 23 na Harin Jirgin Kasan Abj-Kd

  • Rikakkun ‘yan bindigan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun sako sauran 23 dake hannun su
  • Usman Yusuf, sakataren kwamitin shugaban ma’aikatan tsaro ya tabbatar da hakan
  • Yusuf ya sanar da cewa fasinjojin 23 sun shaki iskar ‘yanci ne a ranar Laraba wurin karfe 4 na yammaci

‘Yan ta’adda da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun sako ragowar fasinjoji 23 da suka yi garkuwa da su.

Sakataren kwamitin shugaban ma’aikatan tsaro, Usman Yusuf ne ya tabbatar da hakan kamar yadda Channels Tv ta rahoto.

Yusuf yace an sako fasinjojin da suka kwashe watanni shida hannun miyagun ‘yan bindigan a ranar Laraba wurin karfe 4 na yamma.

Yace kwamitin ne ya karbosu tare da ceto fasinjojin dake hannun ‘yan ta’addan Boko Haram din tun daga ranar 28 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Sabuwar Kotun Soji Za Ta Yanke Wa Wasu Sojoji 68 Shari'a A Sokoto

“Ina farin cikin sanar da kasa da duniya cewa da karfe 4 na yammacin yau Laraba,5 ga watan Oktoban 2022, kwamitin mutum bakwai na fadar shugaban kasa karkashin shugaban ma’aikatan tsaro, Janar LEO Irabor, sun ceto tare da karbar dukkan fasinjoji 23 da Boko Haram suka sace baya farmakin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris na 2022.
“Kasar na mika godiyarta ga sojin Najeriya karkashin shugabancin CDS wanda ya karba tare da jagorancin aikin tun daga farko har karshe. Dukkan hukumomin tsaro da ma’aikatar sufuri ta tarayya sun bayar da gudumawarsu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Cikakken goyon bayan Shugaban kasa kuma kwamandan dukkan jami’an tsaron Najeriya, shugaban kasa Muhammadu Buhari shi yasa aka kai ga haka.
“Mambobin kwamitin nan suna godiya da karamci da damar da aka basu na kasancewa cikin wannan aikin. Allah ya warkar da raunikanmu kuma ya kawo zaman lafiya kasarmu.”

Kara karanta wannan

ASUU Bata Da Wasu Dalilai Masu Kwari Na Ci Gaba Da Yajin Aiki - Buhari

- Yusuf yace.

’Yan ta’adda sun saki sabon bidiyon yadda suka azabtar da fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna

A wani labari na daban, kungiyar ‘yan ta'adda waɗan da suka kai hari kan jirgin ƙasa da ke aiki tsakanin Abuja-Kaduna sun yi baranar tarwatsa Najeriya baki ɗaya.

A wani sabon Bidiyo da yan ta'adda suka sake, sun nuna yadda Fasinjojin jirgin kasa da ke tsare a hannun su ke rayuwa da yadda suke azabtar da su.

A Bidiyon wanda jaridar Leadership ta rahoto, ɗaya daga cikin yan ta'adda ya ce wannan harin da suka kai har ya ta da hankalin kowa to bakomai bane a cikin hare-haren da suke shirin kai wa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng