Matashi Ya Kwarzanta Budurwa Mai Wankin Mota, Ya Tura Mata Kudi Kyauta don Yabawa

Matashi Ya Kwarzanta Budurwa Mai Wankin Mota, Ya Tura Mata Kudi Kyauta don Yabawa

  • Wani ‘dan Najeriya ya fusata wasu mata bayan ya bayyana kyakyawar budurwa dake sana’ar wanke mota
  • Mutumin ya bayyana budurwa ta birge shi ganinta matashiyar tana wanke mota inda ya tura mata kudi a asusun bankinta
  • A yayin kwarzanta budurwar da yaren Yarabanci, ya caccaki ‘yan matan dake da dabi’ar rokon maza kudi

Wani ‘dan Najeriya ya je soshiyal midiya domin kwarzanta wata matashiyar budurwa wacce ke sana’ar wankin mota.

Ya ganta a wurin sana’arta kuma ya tambayeta nawa take karba wurin wanke mota. Tace tana karbar N700 idan ta wanke kowacce mota.

Wankin Mota
Matashi Ya Kwarzanta Budurwa Mai Wankin Mota, Ya Tura Mata Kudi Kyauta don Yabawa. Hoto daga TikTok/@olowosolrem
Asali: UGC

Mutumin da a bayyane budurwar ta birge shi ya kwarzanta ta da harshen Yarabanci inda yake sanar da jama’ar yadda take neman na kanta.

Ya kara da bukatar lambar asusun bankinta kuma ya tura mata kudi don kara mata kwarin guiwa. Mutumin ya kara da kiran mata miyagun sunaye amma masu dabi’ar rokon maza dubu biyu da gaggawa.

Kara karanta wannan

Wannan Shekarar Tazo da Albarka: Budurwar Da Tayi Wata 5 Tana Kwana a Kasa Ta Siya Sabon Gado Dal

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya nadi bidiyon tare da budurwar inda ya wallafa su a shafinsa na TikTok.

Soshiyal midiya tayi martani

Olamideodunafe yace:

“Idan da jami’ar leken asiri ce dake basaja wurin wanke mota?”

Confyjane tace:

“Da fatan kanwarka da matarka suna wannan sana’ar ta wanke mota.”

er3015126548990 yace:

“‘Dan uwa rufe mana baki, wasu daga cikinmu na gwagwarmaya fiye da wannan, ko aikin boyi-boyi wasa ne!”

mhizz purity tace:

“Me yasa zaka taimaketa a maimakon ka aureta saboda gwarzantakar ta. Idan ba za ka iya aurenta ba, toh ka taimaka ka bude mata kasuwanci.”

'Dan Najeriya ya Maka Banki a Kotu kan N27k, An Biya Shi Diyyar Makuden Kudi

A wani labari na daban, wani 'dan Najeriya mai suna Omogaide Mega Gideon, ya shawarci 'yan Najeriya kan yadda zasu shawo kan matsalolinsu da bankunansu bayan ya samu N150,000 da ya maka bankinsa a kotu.

Kara karanta wannan

Dan Achaba Ya Baje Kolin Dankareren Gidan Da Ya Ginawa Mai Shirin Zama Amaryarsa, Hoton Ya Ja Hankali

Gideon yayi martani ne ga wata budurwa a Twitter da ta jajanta yadda aka cire mata N1.1 miliyan daga asusun bankinta ba tare da ta sani ba.

A wallafar da yayi, Gideon ya sanar da cewa ya maka bankinsa a kotu ne bayan yayi kokarin fitar da N27,000 daga POS kuma suka ki fita sannan ya ki sauraron rokon da suka yi masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel