Wannan Shekarar Tazo da Albarka: Budurwar Da Tayi Wata 5 Tana Kwana a Kasa Ta Siya Sabon Gado Dal

Wannan Shekarar Tazo da Albarka: Budurwar Da Tayi Wata 5 Tana Kwana a Kasa Ta Siya Sabon Gado Dal

  • Wata budurwa ta je soshiyal midiya inda ta bada labari mai dadi kan cewa daga karshe dai ta siya sabon gado
  • Ma’abociyar amfani da Twitter @LeratoRSA ta bayyana cewa a cikin shekarar ta fuskanci kalubale kuma hakan yasa take kwana a kasa
  • Abokantata na soshiyal midiya sun taya ta murna kan wannan cigaban da suka samu sannan suka dinga yi mata Allah sam barka.

Farin cikin da zaka shiga bayan ka samu cikar wani daga cikin manyan burikan ka a rayuwa yana da yawa. Wata budurwa ta shiga tsabar farin ciki bayan ta siyawa kanta sabon gado dal.

A wata wallafar da @LeratRSA tayi, ta bayyana cewa ta dade tana kwanciyar a kasa na tsawon wata biyar amma ta samu ta siya gado yanzu.

Kara karanta wannan

Yadda na kwashe shekaru da dama ina jinyar mijina kan ciwon PTSD, Aisha Buhari

Lady Bed
Wannan Shekarar Tazo da Albarka: Budurwar Da Tayi Wata 5 Tana Kwana a Kasa Ta Siya Sabon Gado Dal. Hoto daga TikTok/@LeratRSA
Asali: UGC
“Wannan shekarar bata yi min dadi ba, amma yanzu haske ya bayyana. Nyiyabonga thonga no thixo. A yanzu kuwwa zata fi karfi.”

- @LerotRSA ta kara da cewa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wannan zamanin ba a cika samun gadaje masu arha ba kuma muna taya ta murna domin jajirtacciyar budurwar nan zata shakata yanzu.

Soshiyal Midiya tayi martani

Abokanta na soshiyal midiya sun yi tururuwar cika wallafar da fatan alheri inda suke taya ta murna kan wannan nasarar.

@Current2620 tace:

“Lalela wannan babban nasara ce. Ka yi murnar nasararka, komai kankantarta. Ki kwana lafiya a kan sabon gadon ki ‘yar uwa.”

@Cleeeyo ta rubuta:

“Ni in samu aiki sannan in siyawa kaina sabon gado”

ChifChiduku yayi martani da:

“Ku yi murnan nasara komai kankantar ta.”

@ThullyeNkosi yayi martani:

“Ngiyakibongela cc kuma hakan ya bani kwarin guiwa. Nagode.”

Kara karanta wannan

Idan Na Siya Dankareriyar Mota Kada Kuyi Mamaki, Budurwa ‘Yar Najeriya Da Ke Sana’ar Jari Bola

'Dan Najeriya ya Maka Banki a Kotu kan N27k, An Biya Shi Diyyar Makuden Kudi

A wani labari na daban, wani 'dan Najeriya mai suna Omogaide Mega Gideon, ya shawarci 'yan Najeriya kan yadda zasu shawo kan matsalolinsu da bankunansu bayan ya samu N150,000 da ya maka bankinsa a kotu.

Gideon yayi martani ne ga wata budurwa a Twitter da ta jajanta yadda aka cire mata N1.1 miliyan daga asusun bankinta ba tare da ta sani ba.

A wallafar da yayi, Gideon ya sanar da cewa ya maka bankinsa a kotu ne bayan yayi kokarin fitar da N27,000 daga POS kuma suka ki fita sannan ya ki sauraron rokon da suka yi masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel