Gwamna Ya Karyata Umartar Sojoji Su Suburbudi Duk Ma’aikacin Gwamnati Dake Makaran Zuwa Aiki

Gwamna Ya Karyata Umartar Sojoji Su Suburbudi Duk Ma’aikacin Gwamnati Dake Makaran Zuwa Aiki

  • An yada wani bidiyon dake cewa, gwamna David Umahi an jihar Ebonyi ya fusata da yadda ma'aikatan gwamnati a jiharsa ke yawan makaran zuwa aiki
  • A wani bidiyon da dan gwagwarmaya Chidi Odinkalu ya yada, an ga gwamnan na ba sojoji sanduna tare da umartarsu da su daki ma'aikatan gwamnati a Abakaliki, gwamnan ya yi bayani
  • Gwamnan ya sha bayyana kokensa tare da rufe kofar gidan gwamnati don hana ma'aikatan da suka makara shiga ofisoshinsu

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya bayyana balo-balo cewa, mai amince da batun makaran ma'aikatan gwamnati a jiharsa ba, don haka ya fara daukar mataki.

Wani bidiyon da aka yada a kafar sada zumunta ya nuna lokacin da gwamnan ke ba sojoji bulali da sanduna tare da umartarsu da su suburbudi duk wani ma'aikacin da ke makaran zuwa aiki.

Kara karanta wannan

'Ba Ma'aikata Aka Zane Ba': Gwamna Umahi Ya Magantu Kan Bidiyon Da Ya Bazu Inda Sojoji Ke Wa Wasu Bulala A Gabansa

Umarnin nasa dai ya ba da shi ne kan ma'aikatan gidan gwamnayi a babban birnin jihar, Abakaliki.

Gwamna ya magantu kan cewa ya umarci sojoji su zane masu makaran zuwa aiki
Gwamna Ya Karyata Umartar Sojoji Su Suburbudi Duk Ma’aikacin Gwamnati Dake Makaran Zuwa Aiki| Hoto: Chidi Odinkalu
Asali: UGC

Sai dai, a bayanin da gwamnan ya yi, ya ce sam bai ba da umarnin dukan ma'aikata ba, kawai an dauki bidiyon ne cikin rashin fahimta tare yada shi da mummunan manufa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa, yunkurin ba da bulalin ba komai bane face tabbatar da dakile tsagerun da ke rufe hanyar shiga tashar jirgin sama da sunan kakaba dokar hana fita ranar Talata da 'yan IPOB ke yi.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, an samu tsaiko a jihar Ebonyi a ranar Talata yayin da tsageru ke kokarin kakabawa jama'a takunkumin hana su fita a ranar.

Yadda aka yada bidiyon a shafin sada zumunta

Wani lauya mai rajin kare hakkin bil'adama, Chidi Odinkalu ya yada wani bidiyo a shafin sada zumunta, inda ya zargi gwamnan da umartar sojoji su daki duk ma'aikacin dake makaran zuwa aiki.

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisa Sun Fara Aikin Ruguzawa da Dunkule Ma’aikatu Domin Rage Kashe Kudi

Lauya Odinkalu da ya yada bidiyon a shafinsa na Twitter bai bayyana a daidai ina ne lamarin ya auku ba.

Sai dai, lauyan ya ce lamarin ya faru ne a daidai lokacin da gwamnan ya tafi wani rangadin duba aiki a jihar.

Ya kuma zargi cewa, gwamnan da a yanzu yake neman kujerar sanata a zabe mai zuwa na 2023 ya tsaya tsagin daka domin tabbatar da aiwatar dukan ma'aikatan.

Ya rubuta cewa:

"To, a yau a Ebonyi, @GovDaveUmahi ya tafi duba wani aiki sannan ya umarci sojoji su zane - tabbas su zane - ma'aikatan da suka makara da zuwa aiki. Ba a yi hakan ba, Dave Umahi ya kula da aikin zanewan. Gobe, za a bashi tukuicin kujera a@NGRSenate."

Dan Majalisar Tarayya Ya Yi Kira Da A Rushe Majalisar Dattawan Najeriya Domin A Rage Kashe Kudade

A wani labarin, wani rahoton jaridar Daily Sun ya ce, mamba a majalisar wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Ovia a jihar Edo, Hon Denis Idahosa ya tada wani batu mai ban mamaki a ranar Lahadi 2 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Lambar Girma: Yadda Ake ta Surutu Yayin da Manyan Na-kusa da Buhari Suka Tashi da Matsayi

Denis ya yi kira da a soke majalisar dattawan kasar nan tare da kirkirar majalisa ta bai daya domin rage kashe kudaden tafiyar da gwamnati a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel