Gwamna Umahi Na APC Ya Yi Magana Kan Bidiyon Bola Tinubu Yana Motsa Jiki

Gwamna Umahi Na APC Ya Yi Magana Kan Bidiyon Bola Tinubu Yana Motsa Jiki

  • Gwamnan jihar Ebonyi yace ɗan takarar APC a 2023 ba ya bukatar dole sai ya tabbatar da yana raye
  • Gwamna David Umahi yace rayuwa da mutuwa duk suna hannun Allah rashin lafiya kuma kowa da irin tasa
  • A ranar Lahadi ne Bola Tinubu ya fitar da wani Bidiyo da ke nuna shi yana motsa jiki a kan Keke, yace a shirye yake ya wa Najeriya aiki

Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi yace ɗan takarar shugaban kasa ƙarƙashin APC na nan a raye kuma ba ya bukatar gamsar da mutane cewa yana raye.

Gwamna Umahi ya yi wannan furucin ne yayin hira a shirin Sunrise Daily na gidan Talabijin din Channels tv ranar Litinin.

Gwamna Umahi, Bola Tinubu.
Gwamna Umahi Na APC Ya Yi Magana Kan Bidiyon Bola Tinubu Yana Motsa Jiki Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

Yayin da ake ta cece-kuce kan halin rashin lafiyar da yake ciki, Bola Tinubu, ranar Lahadi, ya yi amfani da shafukansa na kafafen sada zumunta, inda ya saki wani Gajeren Bidiyon kansa yana cewa yana cikin ƙoshin lafiya.

Kara karanta wannan

Yajin ASUU: Wani Gwamnan Arewa Ya Fusata, Ya Dakatar da Biyan Malaman Jami'ar Jiharsa Albashi

Da aka tambaye shi kan ko meyasa Tinubu ya nuna hujjar cewa yana raye ta hanyar nuna kansa yana motsa jiki, Gwamna Umahi yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mutum mai rai ba ya bukatar sai ya gamsar da mutane cewa yana raye. Asiwaju yana raye kuma ba ya bukatar sai ya tabbatar da yana raye."
"Ba mutumin da zai bugi ƙirji ya ce lafiyarsa kalau, haka ba wanda zai ce rashin lafiya ta masa katutu ta ko ina. A wani ma'aunin kuma 'yan Najeriya basu da tausayi, mutumin dake motsa jiki, an ɗauki Bidiyo kuma ana ta watsa wa bai sani ba."
"Bana tunanin ya dace mu maida hankali kan abubuwa irin wannan saboda ita rayuwa kamar Motar Bas ce baka san tashar tsaya wa ta gaba ba. Rayuwa da mutuwa suna hannun Allah."

Meyasa aka samu jinkiri wajen kaddamar da tawagar Kamfe?

Kara karanta wannan

Buhari ga ƴan Najeriya: Nima Ina jin Irin Keburan da Kuke Sha

Dangane da jinkirin da aka samu wajen kaddamar da tawagar yaƙin neman zaɓen APC da rikicin da ya kewaye mambobi 422, gwamna Umahi yace, "Kwamitin kamfe na kara nuna amfanin masu ruwa da tsaki ne kawai."

"Ba wai yana nufin su ne ƙashin bayan nasara a zaɓe ba, asalin siyasa na can ƙasa. A wurina kamfen shugaban kasa yana matakin jihohi, domin a nan ya dace kuma nan zai kasance."

A wani labarin kuma Matsala Ga Tinubu, Ɗaruruwan Mambobin APC Sun Koma Bayan Atiku da PDP a Jihar Arewa

Kwanaki kaɗan bayan fara kamfe a hukumance, jam'iyyar PDP a jihar Bauchi ta samu gagarumin goyon baya.

Wasu dandazon mambobin APC a yankin Duguri sun tabbatar da sauya sheƙa zuwa PDP don mara wa Ƙauran Bauchi baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel