'Yan Bindiga Sun Kashe Malamin Addinin Musulunci, Sun Yi Garkuwa da 'ya'yansa A Kwara
- Wasu miyagun yan bindiga sun kashe malamin addinin Musulinci, Alfa Tunde Aribidesi, a Ilorin jihar Kwara
- Lamarin wanda ya karaɗe kafafen sada zumunta, an ce maharan sun sace 'ya'yan malamin biyu, sun nemi a tattara musu kuɗin fansa
- Kakakin hukumar yan sanda na jihar Kwara, Okasanmi Ajayi, yace har yanzu basu samu rahoton abinda ya auku ba
Kwara - 'Yan bindiga sun kashe wani Malamin addinin musulunci, Alfa Tunde Aribidesi, sannan kuma suka yi garkuwa da 'yanyansa guda biyu a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.
Daily Trust tace lamarin mara dadi ya karaɗe kafar Facebook da wasu kafafen sada zumunta bayan abokin Mamacin, Alfa Lawal Taoheed, ya buga shi, inda ya nemi addu'a da Adalci.
A rubutun da Taoheed ya yi, yace, "Masu garkuwan sun tuntuɓi iyalai, sun buƙaci Miliyan N10m a matsayin kuɗin fansar yaran biyu da suka sace."
Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Kwara, Okasanmi Ajayi, yace har yanzun ba bu wanda ya kai musu rahoton faruwar lamarin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yadda lamarin ya faru ana ruwan sama
Sai dai yayin da jaridar City & Crime ta ziyarci gidan marigayi malamin a yankin Alalubarika da ke ƙaramar hukumar Ilorin ta yamma, ta gano cewa maharan sun tafi da wayarsa.
Wata maƙociyarsa, Misis Nohimat, ta shaida wa wakilin jaridar cewa yan bindigan sun yi awon gaba da wayar Mamacin kuma da ita suka yi amfani wajen neman miliyan N10m kudin fansa.
Ta yi bayanin cewa,
"Sun zo da tsakar dare lokacin ana ruwa suka kutsa cikin gidan da taga bayan fasa ta. Suka kashe shi da wuƙa a gaban manyan yaransa biyu sannan suka yi awon gaba da su."
"Sun nemi matarsa amma ta gudu ta ƙofar baya tun farko zuwa gidan makota domin ta ɓuya."
Wani ɗan uwan Marigayi Malamin, Dakta Rilwanullahi Apaokagi, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya yi kira ga gwamnati ta inganta yanayin tsaro a jihar.
A wani labarin kuma Bello Turji Ya Fusata, Ya Yi Magana Kan Harin da Jirgin Yaƙin Soji Ya Kai Mafakarsa a Zamfara
Sanannen ɗan bindigan nan, Bello Turji, ya nuna damuwarsa bisa harin da jirgin sojoji ya kai gidansa a Zamfara.
Turji yace harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutanensa da dama duk da ya tuba ya rungumi zaman lafiya tsawon watanni.
Asali: Legit.ng