Miliyan N15 Muka Kashe Kan Bikin Aurenmu: Matashiya Yar Najeriya Ta Wallafa Hotuna Da Bidiyoyi

Miliyan N15 Muka Kashe Kan Bikin Aurenmu: Matashiya Yar Najeriya Ta Wallafa Hotuna Da Bidiyoyi

  • Wata matashiya yar Najeriya mai suna Jessica Ayodele ta bayyana cewa sun kashe zunzurutun kudi har miliyan N15 wajen shirya shagalin bikinta a kasar
  • Da take kasafin kudin abubuwa, matashiyar ta bayyana cewa sun biya mai daukar hoto miliyan N1.1 yayin da shirya wajen ya ci miliyan N2
  • Yan Najeriya da suka yi martani sun nuna fargabar abun da zasu zuba a nasu auren idan lokaci yayi

Wata matashiya yar Najeriya, Jessica Ayodele, ta je shafin soshiyal midiya a ranar Lahadi 1 ga watan Oktoba don bayyana makudan kudaden da ta kashe a kan aurenta.

Matar ta bayyana cewa daga ita har mijinta sun kashe zunzurutun kudi har naira miliyan 15 a kan kasaitaccen bikin aurensu.

Mata da miji
Miliyan N15 Muka Kashe Kan Bikin Aurenmu: Matashiya Yar Najeriya Ta Wallafa Hotuna Da Bidiyoyi Hoto: @jessica_xls
Asali: Twitter

Jessica ta bayyana cewa a lokacin da suke shirye-shiryen aurensu a watan Afrilu, duk tunaninta ba za su kashe kudi fiye da naira miliyan 5 ba wajen gayyatar mutane 100 kacal.

Kara karanta wannan

Bidiyon dan takarar shugaban kasan PDP na tikar rawa ya jawo cece-kuce a kafar Twitter

Sun kashe naira miliyan 2.5 kan yawon amarci

Jessica ta bayyana cewa karbar dakin taro a Lagas na da matukar tsada domin yana farawa daga N800,000 kan baki 200 zuwa naira miliyan 4.1 na baki 1000.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta kara da cewar sun kashe miliyan N1.2 da N650,000 kan shirya wajen shagalin biki kawai.

An kashe naira miliyan 1.1 wajen daukar hotuna da bidiyoyinsu. Lamukan kwalba sun ja naira miliyan 1.6, yawon amarci ya ja naira miliyan 2.5. Jessica ta shawarci mutane da su yi daidai ruwa daidai tsaki.

Kalli wallafar tata a kasa:

Ga martanin jama'a a kasa:

@anointed19 tace:

“Damuwata a dukka abubuwan nan shine, kin zabi biyan masu daukar hoto miliyan 1.1 daga miliyan 3, kai Misis Jessica…baku mana adalci ba sam, kun manta aikin mu ne yake hada kundin tarihin bikin.”

Kara karanta wannan

Ka Yi Kokari: Matashi Ya Zana Katafaren Hoton Peter Obi Jikin Bango A Jihar Kaduna, Yan Najeriya Sun Yi Martani

@ObedHailsham ya ce:

“Kirjina !!!"

@ThatPHBoi ya ce:

“Ma’aikacin gwamnati zai dade a unguwa faaaa.”

@Hauwa_L ta ce:

“Da zaran na biya wannan kudin kan aurena kuma ya mutu, zan rufe kofa kuma sai mutanenka sun tattauna kudin fansa dani.”

Tashi Ka Nemi Abun Yi: Fusatattar Matar Aure Ta Dangwararwa Da Miji Kwano Babu Abinci

A wani labarin, masu amfani da TikTok sun yi martani ga wani bidiyo na wata mata da ta gabatarwa mijinta kwano wayam babu abinci a ciki.

A cikin bidiyon, mutumin ya zauna yana jiran a kawo masa abincinsa, kawai sai gashi an dangwaran masa da kwano babu komai.

A cewar matar, mutumin bai da wani aiki sai na tambayar abinci ba tare da fita aiki ko kawo gudunmawar komai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel