Dalibar Jami’a a Najeriya Ta Samu Karuwa, Ta Haifi ’Ya’ya Biyar a Lokaci Daya

Dalibar Jami’a a Najeriya Ta Samu Karuwa, Ta Haifi ’Ya’ya Biyar a Lokaci Daya

  • Wata matashiya mai shekaru 24 kuma dalibar ajin karshe jami'ar ilimin noma ta Michael Okpara a jihar Abia ta haifi 'ya'ya biyar a rana daya
  • Oluomachi Nwoye ta samu jarirai biyar; biyu maza uku kuma mata da misalin karfe 9:15 na dare a jiya Litinin 3 ga watan Oktoba
  • Mahaifiyarta ta bayyana farin cikinta, inda kuma ta nemi tallafin gwamnati da sauran al'umma domin taimaka musu wajen kulawa da jariran, ta ba da lambar waya

Umuahia, jihar Abia - Oluomachi Nwoye, dalibar ajin karshe a jami'ar ilimin noma ta Michael Okpara ta samu karuwar jarirai biyar a rana daya a asibitin tarayya na Umuahia a jihar Abia.

Mahaifiyar Oluomachi ta ce jariran biyar da diyarta ta haifa sun hada da maza biyu da mata uku, kuma ta haihu ne da misalin karfe 9:15 na dare.

Kara karanta wannan

Ku mutunta umarnin kotu ku janye yajin aiki, gwamnatin Buhari ga ASUU

Matashiya ta haifi jarirai 5 a jihar Abia
Dalibar jami'a a Najeriya ta samu karuwa, ta haifi 'ya'ya biyar a lokaci daya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A wani rahoton Vanguard, an ce biyu daga jariran kuma maza na karbar kulawa ta musamman kasancewar an haife su da 'yar matsala.

Mahaifiyar tata, Mrs Priscilla Nwojo ta ce ta shiga farin ciki da samun wannan kyauta daga Allah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai, tace irin wannan baiwa da Allah ke bayarwa na iya zuwa da matsalolin da ba a rasa ba.

Daga nan ne ta nemi gwamnati ta kawo musu tallafi domin samun damar kulawa da wadannan jarirai da suka samu.

Hakazalika, ta ce suna neman taimako daga mutanen da za su iya, inda ta ba lamar waya kamar haka 08035746487 tace a kira domin neman kari bayani.

Martanin jama'a

Victoria Tessy ta yi tsokaci a Facebook da cewa:

"Wannan aiki ne mai girma daga Allah. Ina taya ku murna. Allah yasa hakan ya faru a dangina. Amin."

Kara karanta wannan

Tsohuwar Matar Adam Zango, Maryam AB Yola Tayi Aure, Kyawawan Bidiyoyinta da Ango Sun Dauka Hankali

Christian Grace Nmesomachi tace:

"Ina tayaki murna 'yar uwa. Babu abin da Allah ba zai iya yi ba...Allah zai baki duk abin da kike bukata na kula dasu har girma.

Marvellous Atuliwa yace:

"Ina taya uwa da dangin nan murna."

Doris Adline Asagbra tace:

"Allah abin godiya....ina taya ta murna."

Yadda Wata Baturiya Ta Zo Har Najeriya, Ta Siya Turmi da Tabarya Ta Tafi Turai

A wani labarin kuma, wani bidiyon da wata kyakkyawar mata farar fata na yadda ta siya turmi da tabarya a lokacin da ta ziyarci Najeriya ya ba da mamaki.

A bidiyon da ta yada, matar mai suna Joana ta bayyana cewa tana kaunar cin tuwon doya irin na 'yan Najeriya.

Matar ta ce ta siya turmi da tabaryar ne a Legas domin take iya daka doya domin cin tuwo irin na 'yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.