Yadda Wata Baturiya Ta Zo Har Najeriya, Ta Siya Turmi da Tabarya Ta Tafi Turai

Yadda Wata Baturiya Ta Zo Har Najeriya, Ta Siya Turmi da Tabarya Ta Tafi Turai

  • Joana, wata kyakkyawar mata farar fata ta yada bidiyon turmi da tabarya da ta siya lokacin da ta kawo ziyara Legas a Najeriya
  • A cewarta, ta siya wannan kayan daka ne a Legas saboda tana matukar kaunar cin tuwon doya irin wanda ake yi a Najeriya
  • Bidiyon da ta yada a TikTok ya jawo cece-kuce, jama'a da dama, musamman 'yan Najeriya sun yaba mata da martaba al'adar kasar

Wani bidiyon da wata kyakkyawar mata farar fata na yadda ta siya turmi da tabarya a lokacin da ta ziyarci Najeriya ya ba da mamaki.

A bidiyon da ta yada, matar mai suna Joana ta bayyana cewa tana kaunar cin tuwon doya irin na 'yan Najeriya.

Matar ta ce ta siya turmi da tabaryar ne a Legas domin take iya daka doya domin cin tuwo irin na 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Auren Cin Amana Tsohuwar Matar Adam Zango Tayi, Jaruma Safna Ta Fasa kwai

Budurwa ta zo Najeriya, ta siya turmi da tabarya ta koma turai
Yadda Wata Baturiya Ta Zo Har Najeriya, Ta Sayi Turmi da Tabarya Ta Tafi Turai | Hoto: TikTok/@joannaorou
Asali: UGC

Ta kuma koka da cewa, ta sha siyan tuwo daga gidajen cin abinci na 'yan Afrika mazauna turai, amma ta ce sam babu dadi, kamar ruwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Yan Najeriya sun yaba mata saboda kaunar al'adar Najeriya

Bayan da Joana ta yada bidiyon, jama'a da dama 'yan Najeriya sun yi ca a shashen martani, inda suka bayyana yabo a gareta.

Mutane da yawa sun kira ta matar kirki, sun kuma nuna suna matukar kaunarta.

Kalli bidiyon:

Ga kadan daga martanin mutane

@FemiGrand yace:

"Na fada miki haka tun kafin ki bata hanya zuwa Albaniya....Ke asalin 'yan Najeriya ba wai a alaka ba, daga asalin tushe. Mun san matanmu."

@user6036935716151 yace:

"Yanzu na san daga rayuwarki ta baya ke 'yan asalin Afrika ce, kuma 'yar Najeriya."

@userOBYNO yace:

"Kai! Wannan abu ya yi kyau. Kina da aure ne? Idan baki da aure, ki yi aure a Najeriya."

Kara karanta wannan

Ku mutunta umarnin kotu ku janye yajin aiki, gwamnatin Buhari ga ASUU

@Ghetto Buster yace:

"Kai!Kun ga matar kirki yadi 1000 a irin wannan yanayi."

@user yahaya shuaibu yace:

"Fatan alheri a gareki, ina matukar kaunar yarinya."

@What2have yace:

"Kina da aure ne? Ina ciki."

oyekanmiabiodunol yace:

"Kai kai kai! Wannan abu ne ya yi kyau. Allah ya yi albarka! Kin hadu gaskiya."

@user notym smart yace:

"Ina sonki kuma ina kaunarki."

Abubuwa 9 da Mata Basa So Daga Namiji da Ya Kamata Kowa Ya Sani

A wani labarin, mai amfani da shafin sada zumunta, Thapz ya tambayi mata a Twitter su bayyana abubuwan da ba sa so a jikin namiji, lamarin da ya jawo martani da maganganu masu zafi a Twitter.

Kama daga dabi'u, fita ta jiki har zuwa halaye, mata sun tofa abinda ke zukatansu, inda suka bayyana ababen da basu so game da maza.

Asali: Legit.ng

Online view pixel