Atiku da Wike: Ya Kamata a Canza Wasu Shugabannin PDP Na Kasa, Sanatan Adamawa

Atiku da Wike: Ya Kamata a Canza Wasu Shugabannin PDP Na Kasa, Sanatan Adamawa

  • Sanatan Adamawa ta kudu, Binos Dauda Yaroe, yace akwai bukatar sauya manyan shugabannin PDP na ƙasa
  • Yaroe mai wakiltar mazaɓar da Atiku ya fito, ya roki tsagin Wike su yi koyi da abinda ya faru a 2007 lokacin marigayi Yar'adua
  • Sanatan yace kamata ya yi a aje kowace matsala a gefe har sai bayan Atiku ya lashe zaɓe sannan a ɗauki mataki

Adamawa - Sanata Binos Dauda Yaroe (PDP, Adamawa) yace tabbas ya kamata a canza wasu manyan ofisoshin kwamitin gudanarwa na ƙasa, musamman shugaba da Sakataren PDP na ƙasa.

Sanatan ya ƙara da cewa za'a sauya akalar Ofisoshin ne idan har ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar, ya lashe zaɓen 2023, kamar yadda Daily Truat ta ruwaito.

Iyorchia Ayu.
Atiku da Wike: Ya Kamata a Canza Wasu Shugabannin PDP Na Kasa, Sanatan Adamawa Hoto: Iyorchia Ayu
Asali: Facebook

Ya roki mambobin jam'iyya da suka nuna fushinsu a fili musamman tsagin gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike, su maida takobinsu kube kana su rungumi zaman lafiya.

Sanata Yaroe ya yi wannan tsokaci ne a wurin wani taro da ɗansa, Stephen Binos, ya shirya a Abuja a ƙarshen makon nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jam'iyyar PDP ta tsunduma cikin dambarwa da ta ƙi warwaruwa yayin da tsagin Wike suka tsaya tsayin daka cewa ya zama tilas shugaban jam'iyya na ƙasa, Iyorchia Ayu, ya yi murabus.

Ya kamata mu jingine komai sai bayan zaɓe - Yaroe

Amma Sanata Yaroe mai wakiltar mazaɓar Adamawa da kudu, mazaɓar da Atiku ya hito, yace maimakon matsa wa sai Ayu ya sauka, wanda ya saɓa wa kundin dokoki, kamata ya yi mu yi aiki domin samun nasara a zaɓe.

Yace:

"Atiku ya yi bakin kokarinsa wajen warware rikicin PDP, ya zauna da fusatattun mambobin kuma har yanzun yana tattauna wa da su. Amma wasu mutane na ganin zasu rike jam'iyya da Atiku don ɗaukar fansa kana su yaudare shi."

"A shekarar 2017 lokacin da marigayi Umaru Musa Yar'adu ke takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Ahmadu Ali ne shugaban jam'iyya na ƙasa kuma dukkansu 'yan arewa ne."
"Buƙatar a sauya shugaban jam'iyya na ƙasa daga arewa zuwa kudu bai taso ba sai bayan zaɓe da rantsar da shugaba Yar'adua."

A wani labarin kuma Tinubu Ya Ƙara Naɗa Gwamnan Arewa da Sanata Wamakko a Manyan Mukaman Tawagar Kamfe 2023

Asiwaju Bola Tinubu ya naɗa gwamna Masari na Katsina da Sanata Wamakko a wasu mukaman tawagar kamfen APC.

Wannan na zuwa ne bayan ɗan takarar ya naɗa gwamna Mai Mala Buni da Yahaya Bello duk daga yankin arewa a tawagar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel