Hotunan Wankan Ranar Zagayowar Samun ‘Yancin Kai na Iyalan Shugaba Buhari Sun Kayatar

Hotunan Wankan Ranar Zagayowar Samun ‘Yancin Kai na Iyalan Shugaba Buhari Sun Kayatar

  • Iyalan shugaban kasa Muhammadu Buhari ba a bar su a baya ba wurin daukar wanka mai aji a ranar zagayowar samun 'yancin kan kasar nan
  • A kyawawan hotunan da suka bayyana, an ga iyalansa tare da sirikinasa sun dauka shigar fari da launin kore wanda yake wakiltar kalar Najeriya
  • Hatta Nur Buhari 'yar auta ta bayyana cikin shigar koriyar riga da mayafi launin fari inda ta rike jaka koriya don son Najeriya

Hotunan iyalan shugaban kasa Muhammadu Buhari sun matukar kayatarwa na ranar shagalin bikin zagayowar ranar samun 'yancin kan Najeriya karo na 62.

Iyalan sun yi shigar sutturu launin fari da kore inda suka matukar fitowa suka yi kyau yayin da suka je har filin wasa na Eagle Square.

Kara karanta wannan

Shahada: Halin Da Na Shiga Sakamakon Karban Addinin Musulunci, Wani Dan Jihar Enugu

Iyalan Buhari
Hotunan Wankan Ranar Zagayowar Samun ‘Yancin Kai na Iyalan Shugaba Buhari Sun Kayatar. Hoto daga @fashionseriesng
Asali: Instagram

Kamar yadda @fashionseriesng suka wallafa kyawawan hotunan iyalan, an ga Halima Buhari Babagana da maigidanta, Zarah Buhari Indimi da mijinta Ahmad, Hanan Buhari da angonta Muhammad Turad duk sun fito gwanin sha'awa a filin wasa ana Eagle Square dake Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hatta auta Nur Muhammadu Buhari ba a bari a baya ba, an ga ta cakare cikin shigar riga koriya da mayafi fari inda ta rike karamar jaka koriya wanda hakan suka matukar birgewa.

'Da daya tilo na shugaban kasan, Yusuf Muhammadu Buhari da matarsa Zahra Bayero ma basu sassauta ba, sun fito fes a cikin shigarsu launin kore da fari inda suka karkasce aka kyasta musu hotuna cike da soyayya.

Aisha Buhari Ta Nemi Yafiya Daga Yan Najeriya Kan Rashin Tsaro A Kasa

A wani labari na daban, mai dakin shugaban kasa, Hajia Aisha Muhammadu Buhari, ta bawa yan Najeriya hakuri kan rashin tsaro da tsadar rayuwa da ya jefa yan kasar cikin rayuwar kunci a shekaru bakwai da suka shude.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari Ta Nemi Yafiya Daga Yan Najeriya Kan Rashin Tsaro A Kasa

Ta bayyana hakan ne a ranar Juma'a yayin addu'a da lakca ta musamman don bikin ranar samun yancin kai karo na 62 da aka yi a masallacin kasa a Abuja, rahoton Nigerian Tribune.

A cewar ta, rage darajar naira da cigaba da faduwar darajar naira a kasuwannin canji ya shafi tattalin arziki wacce ta ce ya yi sanadin wahalhalun da yan Najeriya ke fuskanta wurin ilimi, lafiya da harkokin yau da kulum.

Asali: Legit.ng

Online view pixel