Tsaffin Hotunan Hatsabibin Mai Garkuwa Da Mutane John Lyon Yana Bikin 'Birthday' A Cikin Banki Sun Bayyana

Tsaffin Hotunan Hatsabibin Mai Garkuwa Da Mutane John Lyon Yana Bikin 'Birthday' A Cikin Banki Sun Bayyana

  • Yadda ma'aikacin banki ya sauya ya zama mai garkuwa da mutane na cigaba da daure wa wasu yan Najeriya kai
  • Yan sanda sun yi holen John Lyon, gogarman mai garkuwa da mutane a ranar Asabar a Abuja bayan sun dade suna bibiyansa
  • Lamarin ya dauki hankulan mutane a intanet, har ta kai ga wasu tsaffin hotunansa yayin bikin zagayowar ranar haihuwansu sun fito

An yi ta hayaniya a soshiyal midiya a ranar Asabar 24 ga watan Satumba, lokacin da jami'an tsaro suka kama hatsabibin mai garkuwa, wanda ke cikin masu garkuwa da ke adabar mutanen Bayelsa.

Legit.ng ta rahoto cewa yan sanda daga Jihar Bayelsa ne suka rika bin sahunsa, kuma suka kama shi a Abuja.

Kara karanta wannan

Tsagerun Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 5 Da Dan Farar Hula Daya A Anambra

Mai garkuwa Lyon.
Tsaffin Hotunan Hatsabibin Mai Garkuwa Da Mutane John Lyon Yana Bikin Bazday A Cikin Banki Sun Bayyana. Hoto: The Mirror.
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma, tsaffin hotunan wanda ake zargi da garkuwan sun bayyana a intanet, yayin da ya ke bikin zagoyowar ranar haihuwarsa cikin banki tare da abokin aikinsa.

Rivers Mirror ce ta wallafa hotunan a ranar Laraba, 28 ga watan Satumba kuma hotunan sun dauki hankulan mutane a soshiyal midiya.

Martanin wasu yan Najeriya

Ga abin da wasu yan Najeriya suka ce game da hotunan a Facebook:

Fairvor Kay ta rubuta:

"Ban amince ya zama mai goyon bayan Arsenal ba.
"Dan Chelsea ne."

Ordinary Guy ya ce:

"Kulub din Landan kuma ... ban yi mamakin sune Cowboys din Ingila ba."

David Keyz ya ce:

"Na fada cewa babu yadda za a yi wannan mutumin ya rika goyon bayan Chelsea na."

Emmanuel Etochukwu Trust ya ce:

"Dama za su zo Arsenal su gina kansu daga bisani su koma Chelsea su ci kofi."

Kara karanta wannan

An Yi Arangama Tsakanin Yan Sanda Da Yan Kalare A Gombe, Wasu Sun Jikkata

Prince Buchi ya rubuta:

"Yana son ya sanar da mu cewa mai goyon bayan Chelsea zai iya cinye mai goyon bayan Arsenal kamar kek."

Bidiyo: Mai Garkuwa da Mutane dake Watsin Daloli a Soshiyal Midiya Yana Zubda Hawaye a Hannun 'Yan Sanda

A wani rahoton, Bidiyon John Lyon, wanda ake zargi da kasancewa shugaban wata kungiyar garkuwa da mutane, ya bayyana yana zubda hawaye kamar karamin yaro yayin da ya shiga hannun 'yan sanda.

A wani bidiyo, wanda ake zargin da aka fi sani da Lion White, ya bayyana babu riga inda yake sanye da gajeren wando kadai a jikinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164