Tsohon Sarki Sanusi II Ya Ragargaji Gwamnatin APC a Majalisar Dinkin Duniya

Tsohon Sarki Sanusi II Ya Ragargaji Gwamnatin APC a Majalisar Dinkin Duniya

  • Muhammadu Sanusi II ya yi Allah-wadai da yadda Muhammadu Buhari ya bar ASUU tana yajin-aiki
  • Khalifan darikar Tijjaniyya a Najeriya ya zargi gwamnatin APC da rashin ba harkar ilmi martaba
  • Sanusi II ya nuna cewa dole ne gwamnatin Najeriya ta dauki malaman makaranta da likitoci da daraja

New York - Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya gabatar da jawabi a game da sha’anin ilmi a wajen taron majalisar dinkin Duniya da aka yi kwanan nan.

Rahoton Sun ta kasar nan ya nuna tsohon Sarkin Kano ya jagoranci tattaunawa da aka yi a kan yadda za a gyara ilmi ta hanyar amfani da dabarun cikin gida.

Muhammadu Sanusi II ya zanta da hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN, bayan wannan zama da ya jagoranta, inda ya yi bayani a kan sha’anin ilmi.

Kara karanta wannan

Malamin Musulunci Ya Yi Bayanin Hukuncin Yajin aiki, Ya Wanke ASUU Daga Zargi

Basaraken yake cewa za a iya kawo karshen yajin aikin kungiyar ASUU ta hanyar tattaunawa, a ganinsa babu dalilin da za dalibai za suyi watanni babu karatu.

A kula da malaman jami'a - Sanusi

“Ya kamata gwamnati fa fahimci cewa malamai mutane ne; muna fama da tashin farashi kuma albashi bai kai malamai ko ina, dole ne a daraja aikinsu.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ma’aikatan ilmi da malaman lafiya duka, abin da ba ku sani ba shi ne muna ta rasa ‘yan boko, da yawa da suka tafi yin PhD a kasar waje, ba su dawowa.”

- Muhammadu Sanusi II

Sanusi II.ng
Tsohon Sarkin Kano Sanusi II a taron UNGA Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC
“Ana cikin matsala saboda muna neman likitoci a Najeriya, sannan muna bukatar malamai a kasar nan, saboda mun kashe kudi sosai wajen horas da su.”

- Muhammadu Sanusi II

Khalifa yace sai an mutunta ilmi

An ji Khalifan Tijjaniyan yana cewa likitocin da ke aiki a Najeriya duk sun koma kasashen ketare, sannan ya bada shawara cewa a daraja ilmi yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Bayyana Abinda Zai wa 'Yan Najeriya 100m a Fannin Lafiya Idan Ya ci Zabe

Aminiya ta rahoto Khalifa yace malaman makarantu sun samu wasu damammakin, amma suka zabi su koyar a aji, don haka sam bai dace a rika wulakanta su ba.

A cewar Sarkin Kano na 14, wajibi ne a dawo da al’adar da aka sani ta girmama malamai, yace yanzu jama'a ba su ganin kimar malamai saboda ba su da dukiya.

Business Day tace tsohon gwamnan na CBN ya yi bayanin muhimmancin karatun mata. Sanusi II ya dade yana karfafa muhimmancin ilmantar da diya mace.

Ya Halatta Malaman Jami’a Su Yi Yajin-aiki?

Abdallah Gadon Kaya ya yi bayanin hukuncin yajin aikin ASUU da wani Bawan Allah ya yi tambaya ko ya halatta malamai da ke yajin-aiki su ci albashi.

An ji labari fatawar Sheikh Abdallah Gadon Kaya ta nuna ba laifi ba ne ‘yan kungiyar ASUU su daina shiga aji, saboda gwamnati ta iya biya masu bukatunsu.

Kara karanta wannan

Dailin Da Yasa Na Yi Shiru Game da Rikicin Atiku da Gwamna Wike, Saraki Ya Magantu

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng