Dole ku zo nan: ‘Yan Majalisar Najeriya Sun Bukaci Hameed Ali Su Bayyana Gabansu

Dole ku zo nan: ‘Yan Majalisar Najeriya Sun Bukaci Hameed Ali Su Bayyana Gabansu

  • ‘Yan Majalisar tarayya suna bincike na musamman a kan kwangilar da gwamnati ta ba kamfanin Webb Fontaine
  • Kwamitin majalisa ya bukaci Ministan tattalin arziki, CG na gidan Kwastam su zo domin yi masu bayani da kansu
  • Kamfanin Webb Fontaine aka ba kwangilar shigo da na’urorin da kwatsam ke amfani da su wajen laluben kaya

Abuja - Majalisar wakilai da na dattawa sun bukaci Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki na kasa, Zainab Ahmed ta bayyana a gabansu.

The Guardian ta fitar da rahoto a ranar Litinin cewa ‘yan majalisar sun kuma neman yin zama da gwamnan babban bankin CBN, Mista Godwin Emefiele.

Haka zalika ana bukatar ganin Shugaban hukumar kwastam na kasa, Kanal Hameed Ali mai ritaya. Hukumar dillacin labarai ta tabbatar da labarin nan.

Kara karanta wannan

Kwararan Majiyoyi Sun Bayyana Ainihin Dalilin Da Yasa APC Ta Dakatar Da Fara Kamfen Har Sai Baba Ta Gani

Shugaban kwamitin hadaka na majalisar tarayyan Najeriya ya bayyana haka sa'ilin da ya yi wani zama na musamman a birnin tarayya Abuja a makon jiya.

Sanata Francis Alimikhena da ‘yan kwamitinsa na binciken kwangilar da ma’aikatar kudi ta ba kamfanin Webb Fontaine domin taimakawa kwastam.

An ba Webb Fontaine kwangila ne da nufin jami’an kula da kan iyakokin Najeriya su rika amfani da na’ura wajen binciken kayan da ake shigowa da su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majalisar Dattawa
Majalisar Dattawan Najeriya Hoto: @NgrSenate
Asali: UGC

An nemi jami'an gwamnati, sun ki zuwa

Francis Alimikhena yana da ta-cewa a game da wannan kwangila, saboda haka ya nemi ganin Gwamnan babban banki da sauran masu ruwa da tsaki.

Amma da aka yi zama a zauren majalisar, Zainab Ahmed ba ta samu zuwa ba, haka Godwin Emefiele da kuma Kanal Hameed Ali mai rike da kwastam.

‘Dan majalisar yace ba za su saurari wani wakili da aka turo a kan maganar da ta shafi tatso kudin-shiga ba, don haka dole wadanda ake nema su hallara.

Kara karanta wannan

N797bn: Majalisar wakilai ta shiga damuwa, an kashe kudi, an gaza karasa titin Abuja zuwa Kano

Dole ku zo gaban mu - Francis Alimikhena

“Muna so mu ga Minista, Shugaban kwastam, gwamnan CBN, shugaban kungiyar NAGAFF.
Ba mu son ganin wani wakili; muna son daukar mataki ne a kana bin da ya shafi Najeriya. Ana maganar batun kudin-shiga ne a kasar nan.
Kamfanin Webb Fontaine yana da muhimmanci a kan batun, sun samu sosai a kasar nan.

Sabawa dokar zabe

Dazu labari ya zo Hukumar INEC mai gudanar da zabe a Najeriya ta zargi jam’iyyu da sabawa doka a lokacin zabukan shugaban kasa na 2019.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu yace mafi yawan jam’iyyu ba su kawo rahoton kudin da suka kashe ba, kamar yadda doka ta bukata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng