Dakarun Sojoji Sun Ceto Mutane 7 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Jihar Kaduna
- Sojoji sun yi arangama da wasu tsagerun yan bindiga a yayin wani fatrol a kananan hukumomin Birnin Gwari da Chikun da ke jihar Kaduna
- Maharan sun budewa sojojin wuta amma sai suka mayar masu da zazzafan martani wanda ta kai har sai da suka tsere zuwa cikin jeji
- Dakarun sojin sun yi nasarar ceto mutum bakwai da yan bindigar suka yi garkuwa da su cikinsu harda uwa da yayanta hudu
Kaduna - Dakarun rundunar Operation Forest Sanity sun ceto wasu mutane bakwai da aka yi garkuwa da su a yayin wani fatrol a kananan hukumomin Birnin Gwari da Chikun da ke jihar Kaduna.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, jaridar The Cable ta rahoto.
Aruwan yace a wani rahoton aiki da suka samu, yan bindigar sun budewa dakarun wuta a yayin da suke aikin fatrol, rahoton PM News.
Sojojin sun mayar da wutan sannan suka rinjayi yan bindigar, wadanda suka gudu cikin jeji, inda suka bar mutanen da ke tsare a hannunsu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Dakarun sojin sun ceto mutum bakwai masu suna Joseph Ishaku, John Bulus, Gloria Shedrack da yaranta hudu, Jimre Shedrack, Jonathan Shedrack, Angelina Shedrack da Abigail Shedrack.
“Gwamnatin jihar Kaduna ta jinjinawa dakarun sojin sannan ta gode masu kan namijin kokarin da suka yi wajen ceto mutanen.
“An sada mutanen da iyalinsu.”
Yan Bindiga Sun Kashe Dan Sanda Da Wasu 3, Sun Yi Awon Gaba Da Mutane Masu Yawan Gaske A Jihohin Arewa 2
A wani labarin kuma, mun ji cewa tsagerun yan bindiga sun bindige wasu mutane uku sannan suka yi awon gaba da wasu 22 yayin da suka farmaki garuruwan Birnin Gwari da ke jihar Kaduna, Daily Trust ta rahoto.
Harin ya wakana ne a ranar Asabar da misalin karfe 7:30 na yamma lokacin da maharani suna mamaye Hayin Gada na garin Damari da ke gudunmar Kazage, inda suka kashe mutum biyu Sanusi Zubairu da Kabiru Zubairu.
Sun kuma sace mutane 12 sannan suka yi sace-sace a shagunan wannan garin.
Asali: Legit.ng