Babu Wata Jiha da Aka Ba Izinin Mallakar Makamai Masu Sarrafa Kansu, Martanin Fadar Buhari Ga Gwamna Akeredolu
- Gwamnatin tarayya ta bayyana balo-balo cewa, ba a yarje ma kowace jiha ba a Najeriya ta sayi makamai ga 'yan banga ba
- Gwamnan jihar Ondo ya ce zai siya ma 'yan bangan Amotekun na jiharsa bindigogi domin kawo zaman lafiya a jiharsa
- Gwamnan jihar Katsina ya sha kira ga mazauna jiharsa da su mallaki bindigogi domin kare kansu daga 'yan bindiga
FCT, Abuja - Gwamnatin Najeriya ta ce, babu wata jiha a Najeriya da ke da ikon mallakar makamai masu sarrafa kansu kamar dai bindigogi kirar AK47, TheCable ta ruwaito.
Wannan batu na fitowa ne daga wata sanarwa da fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fitar a yau Talata 27 ga watan Satumba.
Gwamnati ta ce, mallakar bindiga kirar AK47 matukar ba a hannun jami'an tsaro bane to tabbas ya saba doka, kuma akwai hukunci a kai.
Sanarwar ta ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Fadar shugaban kasa na son jaddada cewa babu wata jiha, ba Katsina ba, babu wata jiha a kasar ke da iko mallakar makamai masu sarrafa kansu ga hukumomin tsaronsu.
"A karkashin wannan gwamnatin, shugaban kasa ya sha fadi cewa babu wanda aka ba damar daukar AK-47 ba bisa ka'ida ba ko wani makami mai sarrafa kansa, kuma dole a mika su ga gwamnati."
Gwamnan Ondo zai iya ma 'yan Amotekun bindigogi
Wannan sanarwar daga fadar shugaban kasa na zuwa ne bayan da gwamna Akeredolu na jihar Ondo ya ce zai ba 'yan bangan Amotekun bindigogi domin wanzar da zaman lafiya a jiharsa.
Gwamnan ya ce, inda har gwamnatin tarayya za ta ba gwamnatin jihar Katsina damar mallakar bindigogi tare da ba 'yan banga, to babu dalilin hana shi ba 'yan Amotekun bindiga, haka nan Vanguard ta ruwaito.
Sai dai, gwamnati a yanzu ta ce ba Katsina kadai ba, babu wata jiha da aka ba 'yancin mallakar kowane irin makami mai sarrafa kansa.
Gwamnan Katsina: Ku ma ku sayi bindiga ku kare kanku daga 'yan bindiga
A wani labarin, gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya yi kira ga mutanen da ke zaune a yankunan da ke da yawan 'yan bindiga da su mallaki makamai su kare kansu daga ta'addanci.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Darakta Janar na yada labarai ga gwamnan, Abdu Labaran Malumfashi ya fitar, wanda Daily Trust ta samu.
Gwamnan ya ce ba daidai ba ne mutane su mika wuya ga 'yan bindiga ba tare da wani yunkuri na kare kansu ba, lura da cewa tsaro aikin kowa ne.
Asali: Legit.ng