Budurwa Ta Ce Watanni 7 Suka Rage Mata a Duniya. Ta Yada Bidiyonta, Ta Koma Ga Allah

Budurwa Ta Ce Watanni 7 Suka Rage Mata a Duniya. Ta Yada Bidiyonta, Ta Koma Ga Allah

  • Wata budurwa ta jawo sosuwar rai tsakanin 'yan soshiyal midiya yayin da ta ba da kadan daga tarihin rayuwarta
  • Budurwar 'yar kasar Kenya ta ce sauranta watanni 7 a duniya, don haka take neman addu'o'i da fatan karshe mai kyau
  • Jama'a a intanet sun shiga mamaki da jin tausayinta, sun kuma yi mata addu'o'i masu cike da fatan alheri

Budurwar da ta ce sauranta watanni bakwai ta rayu a duniya ta sa zukatan mutane a TikTok sun cika da jimami da tausayi.

Budurwar mai suna Malkai ta yada wani bidiyo a TikTok, inda tace ta gaji kuma ba ta da karfin ci gaba da rayuwa.

Budurwar da sauranta watanni 7 ta rayu ta magantu
Budurwa Ta Ce Watanni 7 Suka Rage Mata a Duniya. Ta Yada Bidiyonta, Ta Koma Ga Allah | Hoto: TikTok/@_malkia1
Asali: UGC

Ta bayyana cewa, tana matukar kokari don iya rayuwa daidai, amma abubuwan sun ci tura. A kalamanta, cewa ta yi:

"Ina da sauran watanni 7 kacal amma ban da karfin ci gaba da tafiya, na gaji, ba zan iya tursasa kaina ba kuma.

Kara karanta wannan

Wanka Kullum Asarar Ruwa Ne: Bidiyon Kyakyawar Budurwar da Tayi wata 1 Babu Wanka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina kokari amma abin ya ci tura kuma wannan kenan. Bazan jima ba a nan."

Bata dai bayyana ko wani abu ne ke damunta da take cewa sauranta watanni 7 kacal a duniya.

Kalli bidiyon:

Martanin jamai'a

Jama'a a kafar sada zumunta sun yi martani, sun bayyana jimami tare da karfafa mata gwiwa.

Ga dai kadan daga ciki:

Zam Nabayaza yace:

"Idan kina jin ba za ki iya ci gaba ba to ki tsaya a can, ki zauna ko ki bar gida ki mika kanki ga 'yan sanda, idan kika isa za su tambayeki ke kuwa kawai kada ki amsa, kiyi shuru.

Nze phoebe yace:

"Ki gudu, ba zan iya cewa nasan me ke damunki ba saboda ke kadai kika san abin da ke damunki, ina jin zafi duk sadda na ga 'yan uwana 'yan Afrika na shan wahala a gidaje."

Kara karanta wannan

Mai kamar maza: Bidiyon budurwa mai tuka tirela ya girgiza intanet, jama'a sun shiga mamaki

nakabonge Victoria tace:

"'Yar uwa daidai ne mutum ya ji ya gaji, amma ba daidai bane mutum ya fidda rai. Kada ki fidda rai har sai kinga abin da ya turewa buzu nadi, nima saura na shekara daya ta tafi."

The Royal Indica yace:

"Daidai ne ki ji haka watarana, da fatan za ki zo gida nan kusa. Watarana yana da kyau mu saurari bugun zukatanmu."

Tsaleliyar Budurwa Mai Tuka Tirela Ta Yada Bidiyo, Ta Jawo Cece-Kuce a Shafin Intanet

A wani labarin, wani bidiyo ya nuna wata 'yar Najeriya da ke tuka tirela, lamarin da ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta.

A shafinta na TikTok, matar ta yada bidiyo masu yawa na yadda take murza babbar mota kamar dai yadda maza ke yi.

A daya daga ciki, an ga lokacin da take binciken kwa-kwaf ga motar kafin tashi. Yayin da take kan hanyar Legas zuwa Ibadan, yaran motarta sun dauki wani bidiyonta, sun bayyana yabo da kambata uwar dakin nasu.

Kara karanta wannan

'Yar kirki: Bidiyon tsaleliyar budurwar da ke taya mahaifiyarta soya garin rogo ya jawo cece-kuce

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.