Halaye 5 Na Dangote, Rabiu, Elumelu da Sauran Hamshakan Attajiran Afrika

Halaye 5 Na Dangote, Rabiu, Elumelu da Sauran Hamshakan Attajiran Afrika

  • Akwai wasu dabi'u da attajiran nahiyar Afrika ke dashi da ba kowa ke dashi ba, wannan kuma ya taimaka musu
  • Ana kyautata zaton wadannan dabi'u da suke dashi suna daga abubuwan da ke kara habaka dukiyoyinsu
  • Kama da ayyukan motsa jiki har zuwa zaman hada harkalla da karatu tukuru, duk na daga dabi'un attajirai

Duk wani mutumin da ya samu daukaka a duniya to dole yana da wasu dabi'u da suka zame masa jiki kuma yake yawan aikata su.

Tatsuniyar cewa, attajirai zaman shantakewa suke yayin da wasu ko kuma dukiyarsu ke kara kanta da kanta ba lallai ya zama gaskiya ba.

Daga attahiran da suka fi kowa kudi a Afrika, akwai darasi mai yawa a tattare dasu, kasancewar mutane masu matukar jajircewa domin samun nasara a rayuwa.

Kara karanta wannan

Bacin rana: Kotu ta tasa keyar wani sarkin gargajiya zuwa gidan yari saboda laifuka biyu

Halaye 5 na attajiran Afrika da ya kamata ku sani
Halaye 5 Na Dangote, Rabiu, Elumelu da Sauran Hamshakan Attajiran Afrika | Hoto: Anna Webber / Stringer
Asali: UGC

Kama daga kan Dangote, mai kudin 'yan Afrika har zuwa kan Tony Elumelu, mai bankin UBA da ma sauran biloniyoyi a Afrika, rayuwar dai itace, basu zauna kamar yadda ake tsammani ba, kamar yadda Legit.ng ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakewa da mai da hankali kan lafiyar kwakwalwa

Biloniyoyi a Afrika basu cika sanya damuwa a kansu ba. Suna da fahimtar cewa, sanya damuwa a rai na iya taba lafiyar jiki da ta aljihunsu, don haka ba sa wasa da kula da lafiyar kwakwalwa.

Sukan yawan kashe kudadensu wajen horar da kai da kwakwalwarsu kan yadda za su kula da lafiyar jiki da ruhinsu.

Misali, mai bankin UBA, fitacce ne idan ana magana a fannin motsa jiki da gina kwanji.

Sadar da kai ga sabbin fuskoki

Duk wani biloniya to dole ya san wani irin mai tarin dukiya a wata duniyar. Daga halayensu shine; ba sa zama su kadai, sukan raba tare da saduwa da sabbin jama'a da ma tsoffin abokan harkalla.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Buhari ya fusata, ya ce shugabannin jami'o'i su bude makarantu a koma karatu

Irin wannan ganawa da sadar da zumuncin juna na taimaka musu wajen samun nishadi tare da tattaunawa abubuwa masu muhimmanci.

Kana sukan gana da wadanda suka fi su kudi, domin kuwa hakan na taimakawa wajen sake samun hanyoyin habaka kasuwa da sanayyar juna.

Dangote kan gaba wajen shige-shige da ganawa da sabbin mutane a kowane a lokaci a jerin attajiran Afrika. An ce mutane rahama ne.

Shi kuwa Tony Elumelu na yawan cewa, kulla alaka da kirki na iya habaka sana'ar da kake, kuma a gaba tabbas za ta amfanar.

Suna zama ne da mutanen da suka san me suke, kuma masu basira

Wadannan attajirai ba sa zama da mutum mara tasiri a rayuwa. Sukan mu'amalanci mutanen da suke da fikira da basira, kuma wadanda suka san me suke yi.

Kuma wannan ya ba su damar iya ganawa tare da sanin fitattun kwararru masu ilimi da fasaha a duniya a bangarori daban-daban.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Duk mai 'bleaching' ya yi hattara da wasu abubuwa 2, gargadin NAFDAC

Mutane ne masu tsari

Attajiran Afrika mutane ne masu matukar tsari, kuma a kodayaushe a shirye suke wajen daukar matakin da zai kai su ga kawo abin ci gaba.

Sukan iya sanin abin da suke bukata kafin su kulla aniyar yinsa, don kuwa tuni suna da abokan da ke taya su tunani kan komai; mutane masu ilimi da nazari.

Su mutane ne da ke akidar nan ta tashi in taimake ka, domin ba sa zaman da zai kai su ga tsoron fara aikata abu mai amfani.

Misali, mai rukunin kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu yakan ce, ya kamata mutane suke nazartar sabbin ayyuka kafin su fara su.

Abokai ne ga littatafai

Attajiran Afrika ma'abota karatu ne, ba sa rayuwa sai da littafi. Sun dauki fahimtar nan ta cewa, makaranta ne shugananni.

Ko dai ka duba rayuwar attajiri Afrika ta Kudu Patrice Motsepe ko na kasar Masar Nassef Sawaris, duk dai abu mafi yawa a rayuwarsu shi ne tsananin kishin kwankwadar ruwan littatafai.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya Sun Gaji da Abubuwan da ke Faruwa a Kasar nan, Atiku

Tsaleliyar Budurwa Mai Tuka Tirela Ta Yada Bidiyo, Ta Jawo Cece-Kuce a Shafin Intanet

A wani labarin, wani bidiyo ya nuna wata 'yar Najeriya da ke tuka tirela, lamarin da ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta.

A shafinta na TikTok, matar ta yada bidiyo masu yawa na yadda take murza babbar mota kamar dai yadda maza ke yi.

A daya daga ciki, an ga lokacin da take binciken kwa-kwaf ga motar kafin tashi. Yayin da take kan hanyar Legas zuwa Ibadan, yaran motarta sun dauki wani bidiyonta, sun bayyana yabo da kambata uwar dakin nasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel