Dan Takarar Shugaban Kasa, Rabiu Kwankwaso Ya Ziyarci Gwamnan APC A Arewa, Sun Sa Labule
- Rabiu Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, ya kai ziyara ga Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Kastina
- Kwankwaso ya ziyarci Masari wanda gwamna ne a jam'iyyar APC a daren ranar Lahadi, 25 ga watan Satumba
- Tsohon gwamnan na jihar Katsina ya ziyarci mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya bude sabuwar sakatariyar NNPP
Jihar Katsina – Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabiu Kwankwaso, ya kai ziyarar ban girma ga gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari.
Kwankwaso ya ziyarci Masari wanda ya kasance gwamna karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a rahar Lahadi, 25 ga watan Satumba.
Kamar yadda ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na twitter, dan takarar shugaban kasar na NNPP ya ce sun tattauna batutuwan da suka shafi kasar a tsakaninsu.
Tun farko dai mun kawo cewa tsohon gwamnanna jihar Kano ya ziyarci mahaifar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, inda ya bude sabuwar Sakatariyar NNPP a garin Daura, da ke jihar ta Katsina.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Hakazalika dandazon jama’a sun halarci taron bude sabuwar sakatariyar ta jam’iyyar mai kayan marmari.
Kwankwaso ya rubuta a shafin nasa:
“Na kai ziyarar ban girma ga abokina, Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, a daren ranar Lahadi.
“Mun shafe lokaci masu ma’ana tare muna tattauna lamuran da suka shafin kasa.”
Shugaba Buhari Ya Fadi Gaskiya Kan Kishin-Kishin Din Ya Nemi a Tube Keyamo Daga Kamfen Din Tinubu
A wani labarin, Fadar shugaban kasa ta yi watsi da rahotannin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi a tsige Festus Keyamo daga matsayin kakakin kwamitin kamfen din dan takarar shugaban kasa na APC.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ya bayyana ikirarin a matsayin kanzon kurege.
Shehu ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya saki a yammacin ranar Litinin, 26 ga watan Satumba.
Asali: Legit.ng